Nijar: Masu tarzomar sakamakon zabe na ci gaba da gudana
February 25, 2021Baya ga toshe wasu manyan hanyoyi a Yamai da kone-konen tayoyi, masu zanga-zangar sun kai farmaki kan gidan wani dan jarida mai zaman kansa, kuma wakilin gidan Rediyon Faransa RFI Moussa Kaka, inda suka farfasa gidan tare da kona wani bangare na gidan.
A baya dai madugun 'yan adawar kasar Mahamane Ousmane da ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 50,3 cikin dari na adadin kuri'un da aka kada, sabanin zababben shugaban kasar Bazoum Mohamed, da hukumar zabe ta bayyana a matsayin wanda yayi nasara da kaso 55,75 cikin dari na adadin kuri'un da akada a yayin zaben na ranar Lahadi da tagabata.
Kawo yanzu kafafen sadarwa na sada zumunta na ci gaba da kasancewa a takaice, bayan da manyan biranen kasar suka fuskanci toshe kafafen intanet a wani yunkuri na takaita zanga-zanga.