1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasha tashen hankula a Kenya

December 31, 2007

Rahotanni daga ƙasar Kenya sun ce mutane aƙalla 124 ne suka rasa rayukansu cikin tarzoma biyowa bayan sanarda zaben shugaba Mwai kibaki da akayi. Sake zaɓen Kibaki ya haddasa tashe tashen hankula na kabilun ƙasar,rahotanni sunce an ƙona gidaje da dama na ‘yan kabilar Kikuyu inda Kibaki ya fito. Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun bada rahotan cewa mutane aƙalla 46 suka rasa rayukansu a birni Niarobi wasu kuma fiye da 40 a Kisumu.

Tuni dai gwamnatin Kenya ta dakatar da gidajen rediyo da telebijin na kasar yaɗa rahotonni kai tsaye bayan sanarda sakamakon zaɓen. A halin da ake ciki dai Ƙungiyar Taraiyar Turai ta baiyana shakkarta game da tabbacin sakamkon zaɓen,wadda ta baiwa Kibaki kuri’u miliyan 4 da digo 58 yayinda Odinga ya samu kuriu miliyan 4 da digo 35. Sakamakon farko dai ya nuna cewa Odinga shi ne ke kan gaba hakazalika kuriar jin rayin jamaa ta nuna cewa Odinga ne ke kan gaba.