1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a birnin Paris da kewaye

November 6, 2005

Kasar Faransa ta fuskanci tarzoma mafi muni a daren jiya tun bayan barkewar tashe tashen hankula da kone kone a unguwanin baki ´yan ci-rani kwanaki 10 da suka wuce. A duk fadin kasar an cunnawa motoci kimanin dubu daya da 300 yayin da aka banka wuta a wasu gidajen. A karon farko wannan tarzoma ta shafi tsakiyar birnin Paris. ´Yan sanda sun ce sun kame mutane kimanin n312 wadanda ke tarzoma da kone kone. Daukacin su dai ´yan asalin kasashen arewacin Afirka ne da kuma na ´yan kudun da hamadar Sahara. A cikin wata hira da yayi da jaridar FAZ dake fita ranar lahadi, ministan harkokin cikin gidan Faransa Nicholas Sarkozy ya bayyana matasa da ke ta da zaune tsaye da cewa wasu daidaikun mutane ne da ba su da imani da kuma doka. A jiya ministan ya ba da sanarwar cewa jami´an tsaro zasu dauki matakan ba sani ba sabo akan matasan. Bayan wani taron gaggawa a karkashin jagorancin FM Dominique de Villepin, Sarkozy ya nunar da cewa gwamnati ta sha alwashin murkushe wannan rikici.