Tashe tashen hankula a Iraq
August 4, 2006Mutane a kalla 23 ne suka rasa rayukan su a Iraqi a sakamakon wasu hare hare da aka kai.
Hari mafi muni shine wanda wani dan kunar bakin wake ya tashi wani bom , a cikin karamar mota yayin daya kutsa kai cikin filin yan kwallo, a arewacin birnin Hadhar.
Hakan yayi sanadiyyar rasuwar yan sanda uku tare da fararen hula 7.
A can garin Mosul kuwa, bayanai sun tabbatar da cewa har yanzu jami´an yan sanda na ci gaba da arangama ne da tsagerun yankin a kai akai.
Wadan nan sabbin tashe tashen hankulan dai sun zo ne , a yayin da babban kwamandan sojin Amurka a Iraqi, Janar John Abizaid ke gargadin kaucewa yakin basasa.
A waje daya kuma, dubbannin mutane yan darikar shi´a ne suka gudanar da wata zanga zangar yin Allah wadai da kasar Israela.
Masu zanga zangar sun kokkona tutocin kasar Israela tare da fadar miyagun kalamai ga shugabannin ta.