Tashe-tashen hankulla a Irak
May 7, 2007Talla
Kimanin mutane 60 su ka rasa rayuka jiya a Irak, a ci gaba da tashe tashen hankulla a sassa daban –daban na wannan ƙasa.
Wanda su ka mutun sun hada ad sojojin Amurika 6 da kuma ɗan jarida ɗaya, a sakamkon harin da yan takife su ka abka masu.
Daga farkon wannan yaƙi,ya zuwa yanzu, a jaimilce, Amurika ta yi assara sojoji 3.374 a kasar Irak.
Saidai duk da haka, fadar gwamnatin White House, na tsaye kan bakan ta na sai ta tsarkake Irak, daga ayyukan ta´adanci.