1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashim Bam ya janyo ta'adi a Pakistan

Umar Saleh SalehAugust 31, 2011

Aƙalla mutane biyar sun mutu sakamakon fashewar bam a Pakistan

Hoto: DW/Faridullah Khan

Jami'an 'yan Sanda a ƙasar Pakistan sun bayyana cewar mutane biyar ne suka mutu, kana wasu 10 kuma suka sami rauni sanadiyyar harin bam da aka ƙaddamar cikin wata mota a yankin kudu maso gabashin ƙasar Pakistan - mai fama da rigingimu. Wani jami'in ɗan Sanda mai suna Mohammad Hashim ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar, bam ɗin ya tashi ne bayan Sallar Eid a cikin wata motar dake ajiye, kuma ba'a san wanda ya ɗana ko kuma ya bar motar ba. Hashimi ya kuma ƙara da cewar, babu wanda ya yi hanzarin ɗaukar alhakin tashin bam ɗin, kuma jami'an 'yan Sanda ba su kai ga yin hasashen maharan ba, ko da shike kuma lamarin ya afku ne a yankin da ke da mabiya ɗariƙar shi'a da basu da rinjaye a ƙasar. Wani jami'in asibiti - mai suna Rasheed Jamali ya ce akwai wata mata guda ɗaya cikin gawarwaki biyar da aka kawo asibitin. Shaidun gani-da ido suka ce akwai motoci da dama da suka ƙone kuma wani gida ma ya lalace sakamakon gobarar da ta taso.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu