Tashin bama bamai a Amirka
April 16, 2013 Rahotani daga Boston dake arewa maso gabashin Amirka, sun tabbatar da tashin wasu bama bamai guda biyu a jiya da yamma inda suka yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 3 yayin da sama da mutun 100 suka samu munayen raunika galibinsu yara da mata a tsakiyar birnin .
Bama baman sun tarwatse ne a bainar jama'a a gefen wata hanya a dai dai lokacin da wasu masu gudun tsrere ke wasaninsu, inji Ed Davis shugaban hukumar 'yan sandan birnin na Boston.
Wani mai magana da yayun fadar White House ta Amirka ya kira tashin bama baman da wani harin ta'addanci, to sai dai kawo yanzu babu wata alamar da ke tabbatar da harin ko na ta'addanci ne.
Jim kadan bayan harin shugaba Barack Obama ya nuna juyayi da kuma alhininsa ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su.
Wannan dai shi ne hari na farko da ya faru a kasar ta Amirka tun bayan hare haren 11 ga watan Satumba da suka wakana wadanda kungiyar Alka'ida ta dauki alhakin kaiwa.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umaru Aliyu