Tashin bama-bamai a Nairobin Kenya
October 13, 2012'Yan sandan uku sun jikata a Nairobi ne bayan da wasu bama-bamai biyu suka tashi a wata unguwar masu hannu da shuni a babban birnin kasar ta Kenya. Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewar an garzaya da wadanda suka jikata asibiti domin ba su kulawa da ta dace. Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin. Sai dai an kaddamar da shi ne a kusa da majami'ar da wani yaro ya rasa ransa a watan da ya gabata sakamakon tashin bam.
Hare-hare sun zama ruwan dare a Kenya tun bayan da sojojin kasar suka kutsa Somaliya a shekarar da ta gabata domin yakar masu tsattsauran ra'ayin musulunci na al-Shabab. Dakarun gwamnatin Kenya sun yi nasarar kwato ikon birnin Kismayo a watan da ya gabata sakamakon nasarar fatattakar 'yan al-shabab da suka yi.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas