Tashin bama-bamai a Pakistan
October 10, 2013Jerin bama-bamai ne suka tashi a wasu muhimman birane huɗu da ke arewa maso yammacin Pakistan a wannan Alhamis (10. 10. 13), waɗanda kuma suka yi sanadiyyar mutuwar a ƙalla mutane tara, tare da raunata mutane 60. waɗannan hare-haren, sun zo ne yini ɗaya kachal bayan da wani jagorar ƙungiyar Taliban ya sanar da cewar, har yanzu a shirye yake domin gudanar da tattaunawar samar da zaman lafiya tare da hukumomin ƙasar. Bam na farko ya tashi ne a wata kasuwar da ke kusa da wani caji ofis a birnin Quetta, mai fama da rigingimu da ke kudu maso yammacin ƙasar, tare da haddasa mutuwar mutane biyar. Bam na biyu kuwa ya tarwatse ne a wani gidan cin abinci da ke Lahore, hedikwatar lardin Punjab, inda fira ministan ƙasar Nawaz Sharif ke da ƙarfin faɗa a ji. A watan jiya ne manyan jam'iyyun siyasar ƙasar suka nuna goyon bayansu ga shawarar da fira minista Sharif ya bayar ta shiga tattaunawar samar da zaman lafiya tare da ƙungiyar Talban, wadda ke tada ƙayar baya a ƙasar tun cikin shekara ta 2007.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Abdourahamane Hassane