Tashin bom a bikin Maulidi a kasar Pakistan
April 12, 2006A ƙalla mutane kimanin 57 suka rasu, wasu da dama kuma suka jikata a wani harin ƙunar bakin wake a birnin Karachi na ƙasar Pakistan. Harin ya auku ne a yayin taron bikin maulidi domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar fiyayyen talikai manzo Annabi Muhammad tsaira da Amincin Allah su tabbata a gare shi. Rundunar yan sanda ta ƙasar ta baiyana cewa an dasa bom ɗin ne a ƙarkashin wata rumfa inda ayarin musulmi mabiya sunni ke gudanar da bukuwan ibadar. Jamaá sun dimauce a yayin da bom ɗin ya fashe a tsakanin mutane kimanin 50,000 waɗanda suka halarci taron maulidin. Jamaár waɗanda suka fusata da wannan alámari sun riƙa ƙona motoci tare da jifar yan sanda da duwatsu. Har ya zuwa yanzu, babu wanda ya baiyana ɗaukar alhakin kai wannan hari. Gwamnati ta bada umarnin rufe dukkanin makarantu a yau laraba domin hana ɗalibai shiga zanga zanga wadda ta gudana a wasu larduna na ƙasar, domin nuna bacin rai da harin bom ɗin. Kantuna da wuraren kasuwanci sun kasance a rufe yayin da aka sami tsaiko na harkokin sufuri a birnin na Karachi.