1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin farashin kayayyakin masarufi a Zambiya

May 31, 2013

Zambiya ta shiga halin ƙunci bisa matakin gwamnati na janye tallafin da ke kan abinci, abin da ya janyo zanga-zanga, inda magoya gwamnati kuma suka far ma masu nuna adawa

Zambia's Patriotic Front (PF) presidential candidate Michael Sata, center, speaks to journalists after casting his vote in Lusaka, Zambia, Thursday Oct. 30, 2008. Zambians elected a replacement for their president who died in office. (AP Photo/Themba Hadebe)
Shugaba Michael SataHoto: AP

Wasu masu fafutukar kare haƙƙin bil adama da 'yan adawa da wani mallamin addini sun ci ɗan karen duka a hannun magoya bayan jamiyyar da ke mulki a Zambia, lokacin da suka mayar da zanga-zangar da suka ƙaddamar kan tashin farashin kayayyakin masarufi zuwa wani Coci, sakamakon soke wanda suka shirya gudanarwa tun farko.

Kamfanin dillancin labarun Faransa AFP ya rawaito cewa, kusan mutane 60 ke cikin wani Cocin da ke wata unguwar talakawa a Lusaka, lokacin da magoya bayan shugaban ƙasa Michael Sata waɗanda su ka cika wata mota ƙirar Bus suka far musu.

Shawarar da gwamnatin ta yanke makonni biyun da suka gabata na janye tallafi kan kayayyakin abinci irinsu garin tuwo, ya janyo ƙorafe-ƙorafe daga al'ummar ƙasar wacce kashi 60 cikin 100n ta, ke fama da talauci.

Haka nan kuma ko a makonni biyun da suka gabata ne ma'yan sanda suka tsare wasu ɗaliban jami'a 31 bisa umurnin shugaban ƙasar bayan da su ma suka yi zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin abincin.

A shekarar 2011 Sata ya zama shugaban ƙasa da gagarumin rinjaye, sai dai kuma masana sun ce wannan sabon yunƙurin na sa zai ƙuntatawa talakawa sosai

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar