Tashin hankali na kassara ilimin yara
September 8, 2016Bikin wannan shekara dai wanda na shekaru 50 ne, na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin farfado da harkokin ilimi a shiyyar Arewa maso Gabas a Najeriya, bayan da rikicin Boko Haram ya dakatar harkokin ilimi a sassan shiyar. A iya cewa dai babban miki da rikicin Boko Haram ya haifar a shiyar Arewa maso Gabas na Najeriyar, shi ne na gurgunta harkokin bunkasa ilimi musamman na Boko wanda kungiyar da ke gwagwarmayar ta haramta shi.
Baya ga hare-hare da aka kai makarantu tare da hallaka dalibai da kuma sace wasu daliban musamman mata, an rufe makarantu da dama a jihohin Borno da Yobe da Adamawa saboda sauke dubban ‘yan gudun hijira a cikinsu. Wannan ba karamin koma baya ya haifar ba a harkokin ilimi a shiyar Arewa maso Gabas din a Najeriyar, yankin da dama ya kasance mafi koma baya a bunkasar ilimi tsakanin takwarorinsa na kasar. Iyaye da yara da masu ruwa da tsaki na ci gaba da bayyana damuwa kan rashin zuwan yaran makaranta musamman a jihar Borno, inda wani bawan Allah a Maiduguri ya ce rashin zuwan ‘ya‘yansa makaranta ya jefa su cikin wani hali.
Yanzu haka dai Sarkin Gombe Abubakar Shehu Abubakar ya fito da shirin daukar nauyin karatun yara marayu, a inda yanzu ake shirin daukar yara kusan 2.000 a Gombe da Kwami bayan sama da 1.000 da ya dauka a shekarar karatun bara, abin da ake ganin zai taimaka gaya wajen habaka harkokin ilimin a shiyar ta Arewa maso Gabas a Najeriyar.