Tashin hankalin ƙabilanci a Kenya
August 22, 2012Talla
A kasar Kenya aƙalla mutane 48 suka hallaka a wani fadan ƙarbilanci, tsakanin wasu ƙabilu biyu. Wannan shine tashin hankalin ƙabilanci mafi muni tun bayan tashin hankalin da ya biyo bayan zaben ƙasar shekaru hudu da suka gabata. Babban jami'in yan sanda a yankin Joseph Kitur yace, lamarin ba ken gani, daga cikin wadanda aka hallaka har da mata 31, yara 11, da wasu mazaje 6. Faɗan ta farune tsakanin ƙabilar Pokomo da ta Orma, wadanda ke wani ƙayen a ƙasar ta Kenya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Abdullahi Tanko Bala