Tashin tantabaru lokacin rantsar da shugaban Najeriya
September 30, 2015Tun kafin yakin duniya na biyu akwai kokarin nuna zaman lafiya ta hanyar 'daga tantabaru, wanda farare aka fi saki sama, domin mutane su nuna sha'awarsu ga zaman lafiya da dorewar jindadi ga mutanensu. Bayan yakin duniya, da aka kafa Majalisar Dinkin Duniya, daga cikin tambarin da ta yi, tantabara ta dora a tsakiya. Wanda ya ke nufin cewa tana fatan bayan yakin a samu zaman lafiya a duniya gaba daya. Dan haka sai aka dauki fararan tantabaru a matsayin wata alama ko symbol, a Turance, wanda mutane za su fahimta cewa gwamnati tana tattare da tsawatarwa jama'a wajen kawo zaman lafiya da kuma ciyar da arzikin kasa gaba. To bayan an yi yakin duniya sai ya kasance shugabanni a yayin da ake yin taro ko kuma wani muhimmin taro da ya shafi kamar zagayowar shekara ta ranar da aka samu 'yancin mulkin kai, ga kasar da aka mulka, ko kuma ranar bikin kaddamar da sabuwar gwamnatin kasa. Ko kuma bayan an gama yaki ana son a nuna cewa zaman lafiya ake bukata, sai a saki fararan tantabaru sama dan tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.