1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rawar malaman addini a siyasar Najeriya

September 27, 2022

Masana na fashin baki kan irin rawar da malaman addini za su iya takawa don ganin an gudanar da ingantacciyar zabe a shekarar 2023 a Najeriya.

Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Hoto: Katrin Gänsler

A yayin da miliyoyin 'yan Najeiya ke shirin shiga filin yakin neman zaben shugabanni, rawa ta shugabannin addini na dada daukar hankali cikin kasar da a baya ta fuskanci rigingimun addini. Shekara da shekaru malaman addini na taka rawa ta kan gaba a lokuta na zabuka a Najeriya.

Hawa mumbari wajen neman goyon bayan gwanaye na siyasa walau a masallatai ko kuma coci-cocin kan dauki hankalin  miliyoyin mabiya a cikin sunan addini, sai dai kuma ana zargin malaman da ingiza rikici da kila fifita na goro wajen nunin goyon bayan na siyasa.

Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad AbubakarHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Abun kuma da manya na shugabannin addinai a kasar ke neman sauyawa tare da wani taron da ya gargadi shugabannin addinan ya zuwa neman dai dai, kuma kama daga mai alfarma sarki na musulmi ya zuwa ga shugaban kungiyar kiristocin Najeriyar, karatu na gargadin yayi sama da nufin kaucewa siyasa ta mumbarin mai tasiri.

Tun ba'a kai ga ko'ina ba dai dama addinin yai nisa a zuciya ta masu siyasa da kila ma 'yan zabe na kasar bayan yanke hukuncin wasu jam'iyyu na tsaida 'yan takara  daga addini guda daya.Gabanin yakin neman zabe, akwai dai tsoron cacar-bakin na iya rikidewa ya zuwa babban rikici cikin kasar da ke fuskantar jerin rigingimun rashin tsaro kama daga arewacin kasar zuwa ga kudancinta.

Arch Bishop Kardinal John Onaiyekan Hoto: DW/Christoph Strack

Koma ya take shirin kayawa a tsakanin malaman addinin da ke fatan mallaki na masu siyasar da kuma masu siyasar da ke bukatar amfani da malaman da nufin cika buri a cikin yakin neman zaben dai, a baya an sha da gumin goshi a kokari na warware lamura bayan rikidar rikici na siyasa ya zuwa fito na fito da sunan addini .

Ana zargin kokari na komawa ta kungiyoyin addinai, sabuwar kafar matsa lamba ta siyasa maimakon hanyar jagorantar al'umma ya zuwa tsirar da suke da babban buri.

Amma a fadar Ravaran Yakubu Pam da ke zaman tsoho na shugaba na kungiyar Kiristocin arewacin kasar CAN  ana bukatar karatun nutsuwa da nufin kaucewa rikicin da ke iya daukar 'yan kasar zuwa ga makwabtan da ba su da karfin iko na tallafi.

Shi kansa yakin basasar da ya kai ga asarar rayuka miliyan kusan biyu a shekaru hamsin da doriya ana kallon tushensa daga kokari na nuna fifikon addinin da kabila cikin siyasa ta kasar mai zafi.