1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gamsuwar kasashe kan yarjeniyar nukiliyar Iran

Gazali Abdu Tasawa/ZMAJuly 14, 2015

Bayan kai ruwa rana an cimma yarjejeniya kan batun nukiliyar Iran tsakaninta da manyan kasashen yammacin duniya bayan tattaunawa ta sama da watanni 20

Atomgespräche in Wien abgeschlossen
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Neubauer

Wannan yarjejeniya dai ta tanadi takaice shirin nukiliyar kasar ta Iran a tsawon shekaru masu zuwa, a yayin da daga nasu bangare manyan kasashen duniya za su rinka janye sannu a hankalin matakan takunkumin da suka kargama wa kasar. Haka zalika ta kuma tanadi bai wa jami'an hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA damar gudanar da bincike a tashoshin nukiliyar kasar ta Iran.

Da ta ke jawabi jim kadan bayan sanya hannu akan wannan yarjejeniya ministan harakokin wajan Kungiyar Tarayyar Turai Federika Mogherini ta bayana lamarin da cewa wata rana ce ta tarihi.

"Yau rana ce mai cike da tarihi, muna farin cikin sanar da ku cewa mun cimma yarjejeniya dangane da makamashin nukliyar Iran cikin mutunci da darajanta juna. Mun gabatar da abin da duniya ta sa ran gani wato bangarorin biyu sun bayar da kai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya. Wannan rana ta kasance ta tarihi ce kuma saboda mun hada kai wajen girka sharuddan da zasu sanya yarda a tsakaninmu, abin da ya bude sabon babi ga dangantakarmu".

Kasashen duniya dai na ci gaba da bayyana farin cikinsu da cimma wannan yarjejeniya. Ministan harakokin wajen kasar Birtaniya Philip Hammond ya bayyana fatan ganin yarjejeniyar ta kawo sauyi a cikin huldar kasar ta Iran da makobtanta na kusa dama kuma sauran kasashen duniya.

A tsawon shekaru da dama dai takunkumin da kasashen duniya suka garkama wa kasar ta Iran ya tanadi haramata sayar mata da makamai. Sai dai a yanzu bayan cimma yarjejeniyar, kasar Rasha ta bakin ministan harkokin wajenta Sargeyi Lavrov ya bayyana fatan ba su damar soma samar wa da kasar da makamai daga yanzu inda yayi karin bayani yana mai cewa.

Hoto: Reuters/L. Foeger

"Dangane da takunkumin da ake sanya na makamai, tare da China mun yi kira da ya kaance daga cikin na farkon da za a dage, to amma abokan huldarmu na Iran ne ke da hurumin yanke hukunci kan wannan, kuma sun cimma matsaya. Da farko kasashen yamma sun hakikance kan barin takunkumin na tsawon shekaru takwas zuwa goma, amma a yanzu an amince da shekaru biyar, wanda cikin wadannan shekaru muna iya aika masu makamai bisa tanadin sharuddan da kwamitin sulhu na Majalissar Dinkin Duniya ya gindaya".

Tuni dai wannan yarjejeniya ta soma yin kyakyawan tasiri a kan darajar kudin kasar ta Iran kamar yanda wannan mutun mazaunin birnin Tehran ya shaida.

Sai dai yanzu haka wannan yarjejeniya ba za ta soma aiki ba gadan gadan sai bayan hukumomin kasar Amirka da ma na kasar ta Iran da kuma komitin sulhu na Majalaissar Dinkin Duniya sun yi nazarin kwakwab a kan abun da ta kunsa tare da bayyana matsayinsu.