1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAfirka

Tasirin Cocin Katolika a Chadi

Mouhamadou Awal Balarabe Blaise Dariustone/SB
February 3, 2026

A babban birnin Chadi, manyan bishop-bishop na kasashe shida na yankin tsakiyar Afirka sun kammala taro karo na 13 na kungiyarsu ta ACERA, inda suka yi nazari tare da bayyana alkibla da Cocin Katolika za ta fusaknata.

Ginin Coci
Ginin CociHoto: Sodiq Adelakun/REUTERS

Yawancin mabiya cocin Katolika na Chadi sun bayyana cewar darikarsu ba ta samun angizo sosai a fagen addini a kasar idan aka kwatanta da Musulunci. Sannan sun zargi darikar da rashin kulawa da daukar matakai ko matsaya a duk da wasu munanan halaye da bangaren ikon Chadi ke nunawa.

Tasirin Cocin

Ginin CociHoto: Wirestock/Pond5 Images/IMAGO

Hasali ma dai, wadannan Kiristocin suna son ganin cocin Katolika da ke Chadi na tasiri kamar yadda cocin Katolika da ke Kwango ke yi a karkashin babban taron bishop na Kwango (CENCO), wanda a lokuta da dama ke daukar matsayi kan batutuwan da suka shafi siyasa.

Sai dai Samuel Mbaïrabé Tibibgar, Bishop na Koumra a kudancin kasar Chadi ya ce wannan sukar ba ta da tushe da makama saboda cocin Katolika da ke Chadi na taka rawar gani.

Irin wannan ra'ayi shi ne ma masanin kimiyyar siyasa na Chadi Evariste Ngarlem Toldé, ya yarda da shi, inda ya jaddada cewa, Cocin Katolika na gudanar da shirye-shirye da aikace-aikace da yawa a fannin zamantakewar al'umma a tsawon tarihinta.

A bisa ga kidayar jama'a ta karshe da aka gudanar, mafi yawan al'ummar Chadi Musulmi ne, inda take da kusan kashi 55% na Musulmai da kuma kashi 41% na Kiristoci. Sannan daga cikin wadannan Kiristoci, adadin mabiya darikar Furotesta ko Evangelic ya dan zarta mabiya darikar Katolika. Me yiwuwa, wadannan alkaluma ne ke bayyana raunin tasirin Cocin Katolika a Chadi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani