1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arzikiNijar

Tasirin da sauke farashin man fetur zai yi a Nijar

Salissou Boukari MAB
July 18, 2024

Gwamnnatin Nijar ta sanar da rage farashin man fetur domin amsa kiraye-kirayen da kungiyoyi da al’umoma suka yi mata. Sai dai wasu 'yan kasar na ganin cewar har yanzu da saura rina a kaba don rayuwa ta yi tsada sosai.

Wani guidan mai a birnin Niamey na Jmhuriyar Nijar
Wani guidan mai a birnin Niamey na Jmhuriyar NijarHoto: DW/M. Kanta

Sanarwar rage farashin man fetur ta fito ne kwatsam a matsyin bazata, duk da cewa gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kafa kwamitin da ke nazari rage farashin kudin man. Sanarwar ta ce an rage farashin man fetur daga CFA dari da dala takwas zuwa dari ba tamma daya yayin da man Diesel aka rage daga  dari da talatin da uku da tamma uku zuwa dari da ashirin da uku da tamma uku inda dukanninsu aka samu ragowa ta tamma hamsin.

Karin bayani: Nijar za ta sayar wa Najeriya man fetur

Wani daga cikin masu manyan motocin daukan kaya duk da bai so a nadi muryarsa ba, ya ce ragin zai musu amfani sosai domin suna sayan man diesel har lita dubu, saboda haka za su ga ragi a zahiri. A fannin 'yan kungiyar masu motocin jigilar jama'a ta bakin sakataransu Alhaji Mounkaila Oumarou kuwa, sun yaba wannan ragowa da aka samu:

Karin bayani: Nijar: Sauye-sauye a aikin hakar man fetur

Cuwa-cuwar mai za ta iya ja baya a Maradi bayan sauke farashin feturHoto: picture-alliance/ZB

Ita ma kungiyar kwadago ta UTTAN ta masu harkokin sufuri da Gamatie Mahamadou ke jagoranta ta yaba ragin man fetur da gwamnati ta yi. Amma sun yi zaton cewar rage farashin zai fi haka. Su ma direbobin Taxi ba a bar su  abaya wajen bayyana ra'ayinsu kan wannan mataki ba. Sai dai  masu nazarin harkokin yau da kullum irin su Ari Boulama da ke koyar da aikin hannu ya ce ba rage kudin mai ne yakama a yi ba.

Karin bayanFitar da man Nijar ta Benin cikin gagarii: 

Kaman yadda mutane da dama suka yi fatan ganin ragin farashin ya fi haka, amma akasari jama'a sun yaba matakin da hukumomin na Nijar suka dauka, saboda a ganinsu alamu ne na sauraron kukan al'umma wadanda suke ganin cewar nan zuwa gaba za a iya samar da saukin rayuwa ga al'umma ta kasa baki daya.