1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin juyin mulkin Nijar a jaridun Jamus

Usman Shehu Usman MAB
August 4, 2023

Jaridu suka ce hambarar da Shugaba Bazoum da sojojin Nijar suka yi ya mayar da hannun agogo baya a yunkurin Jamus na dawo da dakarunta da ke Mali zuwa kasar tare da dagula lissafin Faransa a fannin jibge sojojinta.

Shugaba Bazoum da shugaban gwamnatin Jamus Scholz a birnin YamaiHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce batun janyewar sojojin Jamus daga arewacin Mali ya fada cikin hatsari, inda ta ce tun bayan juyin mulkin da ya faru a Jamhuriyarar Nijar lamaru suka dagule musu. Dama kasar Jamus ta shirya kwaso sojojinta daga Mali i zuwa Jamhuriyarar Nijar. Wani jawabin ma'aikatar harkokin wajen Jamus da aka fitar ya nuna cewa wannan tsarin ya sha ruwa, domin Nijar da ake ganin kamar wurin jibge sojojin kasashen Yamma ta zama kasar da ba tabbas. Sanarwar ta ci gaba da cewa duk wani aikin da dakarun kasashen Yamma suka jima suna yi a Nijar, aikinsu ya zama na banza saboda an share hukumomin dimokuradiyya bayan tsare shugaba Mohamed Bazoum wanda aka zaba bisa tsarin dimokuradiyya.

Juyin mulkin Nijar ya mamaye kannun labarai

Janar Abdourahmane Tchiani ne ke jagorantar gwamnatin mulkon sojan NijarHoto: REUTERS

Jaridar ta Süddeutsche Zeitung ta kuma duba wani bangare na juyin mulkin Nijar, inda ta ce kasar ta kubuce daga hannun Faransa da ke zama kasa ta karshe da ke karkashin hamatar Faransa a yankin Sahel. Jaridar ta ci gaba da cewa sabuwar guguwar siyasar da ke faruwa ta nuna karara yadda Faransa ta rasa madafa a nahiyar Afiirka. Faransa ta kwasoo 'yan kasarta domin dawo da su gida. Jaridar ta yi kiyasin cewa 'yan kasar Faransa 500 izuwa 600 sun fice daga Nijar. Sannan akwai Jamusawa kimanin 100 da ke kan layi don a fitar da su daga Nijar i zuwa kasaru.

Taron Rasha da Afrika na ci gaba da daukar hankali

Shugba Putin na Rasha da takwarorinsa na Afirka sun tattauna batutuwa da damaHoto: Mikhail Tereshchenko/TASS/dpa/picture alliance

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung wacce ta yi sharhi kan taron Rasha da kasashen Afirka ta ce, taron wanda aka yi domin karfafa huldar tattalin arziki tsakin Rasha da nahiyar Afirka ta kasance wata dama ga Rasha ta nuna wa Afirka illar babakeren kasashen mulkin mallaka. Jaridar ta kara da cewa, daga irin jawaben da suka fita daga bakin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, za a fahimci cewar a zahiri an mayar da hankali ne kan yadda kasashen da suka yi wa Afirka mulkin mallaka suka mamaye arzikin nahiyar, kuma har yanzu suna daukar kansu a matsayin iyayen Afirka.

Rasuwar Bedié ya sa an yi waiwaye a Côte d'Ivoire

Tsohon shugaban Côte d'Ivoire Henri Konan Bedie ya rasu sakamakon rashin lafiyaHoto: Diomande Ble Blonde/AP Photo/picture alliance

die tageszeitung: ta yi sharinta ne kan mutuwar fitaccen dan siyasa na Côte d' Ivoire Henri Konan Bédié mai shekaru 89 da haifuwa. Jaridar ta ce shi ne daya daga cikin mutune biyu da suke da kusanci da tsohon shugaban kasar Félix Houphouët-Boigny. Saboda haka da Bédié aka yi ra damawa daga shekarar 1960 har izuwa 1993 a cewar jaridar, inda ya ci gaba da zama kan mulki har sai da sojoji suka yi masa juyin mulki a shekarar 1999. Ya gaji C°ote d' Ivoire a matsayin kasa mafi zaman lafiya a Afirka, amma kuma bayansa kasar ta fada cikin yakin basasa.