Tasirin kalaman Janar Babangida a siyasar Najeriya
February 21, 2025
Bayan kwashe shekaru 32 ne tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kansa ya warware takunkumin da ya sanyawa bakinsa a kan zaben 12 ga watan yuni da ya sauya alkiblar siyasar Najeriya. Bayan amsa cewa lallai marigayi Cif Moshood Abiola ne ya lashe zabe, ya kuma dauki nauyin dukanin abubuwan da suka faru. Dr Yunusa Tanko, dan siyasa da ke cikin wadanda suka yi gwagwarmayar soke zaben June 12 a shekarar 1993 ya ce Janar Babangida ya tayar da fami ne a kan mumunan raunin da zaben ya yi a Najeriya.
Karin bayani: Makomar Jam'iyyun adawa a Najeriya
Ko da yake kalaman da Janar Babangida ya yi ba sabon abu ba ne daga tunanin mafi yawan al'ummar Najeriya da suka yi imanin cewa Cif Abiola ne ya sanya fuskantar tayar da karaya baya musamman daga bangaren 'yan kabilar yarabawa. Amma Farfesa Abubakar Umar Kari, masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abuja.ya ce akwai abubuwan da za su iya sauyawa a fagen siyasar Najeriya.
Karin bayani: Siyasar sauya sheka a Tarayyar Najeriya
Mafi yawan al'umma Najeriya na kallon Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin mazari da ba a san gabanka ba, amma duk da cewa shi soja ne, Dr Kabiru Danladi Lawanti na ganin cewar akwai darussa daga abin da ya faru. Soke zaben na June 12 dai ya sanya Najeriya shiga mataki na lallashi ga kabilar Yarabawa a 1999, inda aka lalubo da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo a kokari na yi wa lamarun saiti.
Karin bayani:Sharhi kan siyasar ubangida a Najeriya
A yayin da kalaman Janar Babangida suka kara fito da abubuwa a fili, zaben na June 12 zai ci gaba da kasancewa wanda ba za a manta shi ba a tarihin Najeriyar musamman a yanzu da kasar ta kara dagewa a kan mulkin dimukuradiyya.