1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin kotun ICC ga kare hakkin dan Adam a Najeriya

Uwais Abubakar Idris YB
July 17, 2018

Shekaru 20 ke nan da kafa kotun kasa da kasa da ke hukunta wadanda suka aikata miyagun laifuffuka da take hakkin dan Adam da cin zarafin jama’a wato kotun ICC.

Symbolbild Internationaler Strafgerichtshof Den Haag
Hoto: Getty Images

Kotun da aka kafa a ranar 17 ga watan Yulin 1998, ta kasance muhimiyyar kafa ta rage wadannan matsaloli. Shekaru 20 dogon lokaci ne ga rayuwar duk wata hukuma irin kotun kasa da kasa ta ICC, wacce ta fuskanci kalubale mai yawa a gudanar da aiyukanta. Najeriya daya ce daga cikin kasashe 118 da suka amince da kotun. Malam Auwal Musa Rafsanjani shugaban hukumar gudanarwa ta kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International a Najeriya ya bayyana muhimmancin kotun da ta fara aiki tun a 2002. Ya ce samun kotun ya taimaka wajen wayar da kan jama'a kan take hakkin bil Adama.

To sai dai kotun ta gamu da zarge-zarge na zama wacce ta fi mayar da hankali a kan hukunta shugabanin kasashen Afirka, abin da ya sanya ta fusknaci ficewar wasu kasashe da dama. Dr. Kole Shettima jigo a kungiyar CDD mai bunkasa dimukuradiya wacce ita ce sakatariyar kotun a Najeriya ya yi karin haske a kan lamarin: Ya ce kotun ta rage armashi saboda yadda aka ga ta mayar da hankali kan Afirka mafi akasari.

Alkalai a kotun ta ICC da ke birnin HagueHoto: AP

Kotun ta ICC dai ta karbi koke-koke har 131 daga Najeriyar a kan batutuwa na zargin aikata miyagun laifuffuka na take hakkin jama'a da ake zargin jami'ai da aikatawa. Kama daga batun Boko Haram ya zuwa ‘yan IPOB da kashe-kashen jihar Plateau da ma Adamawa. Hajiya Saudat Shehu Mahdi ita ce shugabar kungiyar kare hakokin mata da cin zarafinsu ta WRAPA, ta bayyana cewa kotun ta taimaka wa mata musamman yadda ake bayyana laifin fyade a matsayin babban laifi.

Duk da tasiri da kwarjinin kotun rashin saka ta a dokokin Najeriya na zama babban cikas ga samun cikakken amfaninta ga kasar, abin da ake ci gaba da gwagwarmayar fatan ganin faruwarsa. Shugaban na Najeriya dai Muhammadu Buhari na zama cikin masu jawabi a wajen bikin cikar kotun shekaru 20 da kafuwa.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani