1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

120711 Nigeria Konflikte

July 13, 2011

Yayin ziyararta a Najeriya shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel za ta ba da fifiko ne ga dangantakar tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen biyu da ke fuskantar tarnaƙi daga rikice-rikicen Najeriya

Angela Merkel tana gaisawa da jami'ai yayin rangadin AfirkaHoto: picture alliance / dpa

Babban abin da shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel za ta fi mai da hankali akai yayin ziyararta a Tarayyar Najeriya shine ƙarfin tattalin arziƙi da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. A lokacin da Najeriya ke zaman muhimmiyar abokiyar ciniki a fannin sayar wa Jamus man fetur, a ɗayan hannun kuma tana zaman muhimmiyar kasuwa ta fasahar Jamus. To amma akwai kamfanonin Jamus da dama da ke bayyana shakkun shiga wannan ƙasa sakamakon tabarbarewar halin tsaro a wasu yankunan ƙasar. A ma cikin shekaru goma da suka gabata dubun dubatan rayuka daga ɓangarorin al'uma daban daban ne aka yi asararsu a Jihar Filato da ke tsakiyar Tarayyar ta Najeriya.

Dabarar samar da zaman lafiya a Filato

A jihar ta filato zaka samu matasa maza da mata, musulmi da krista daga ɓangarorin daban daba na al'uma da suka tsai da shawarar ɗaukar matakin bai ɗaya domin samar da zaman lafiya. Manufarsu dai ita ce kau da gaba daƙkiyayyar da ke akwai tsakanin Hausawa da Fukani a ɓangare ɗaya da ɓangarorin krista daban-daban a ɗayan ɓangaren-waɗanda kafin shekaru goma da suka gabata suke zaman girma da arziƙi da juna. A lokacin da yake bayyana ra'ayinsa game da wannan rikici babban limamin birnin Jos. Sheikh Balarabe Dawud ya nuna irin banbanci da musulmi musammam Hausawa ke fuskanta a jihar Filato.

Yace:" Ana ci gaba da hana mu shiga a dama da mu a aikin tafiyar da wannan birnin da muka asasa muke kuma zaune a cikinsa. An ƙaddamar da yaƙi ne bisa nasarar da muka samu a zaɓe. Wannan shine dalilin tashin hankalin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa".

A nan Sheikh Dawud yana nuni ne da zaɓen ƙaramar hukuma da ya gudana a ƙarshen watan Nuwamban shekarar 2008 wanda shine musabbanin ɓarkewar rikicin da aka fuskanta a baya-bayan nan a birnin Jos.

Rawar da addini ya taka a rikicin Filato

Unguwar Musulmai da Kristoci a birnin JosHoto: DW

Musulmi dai a nasu ɓangaren sun ƙi su fahimci dalilin da ya sa Krista ya lashe zaɓen da zai kai shi ga riƙe mukamin shugaban karamar hukuma da ke tattare da muhimmacin gaske wajen tsai da shawara akan yadda ya dace a raba kuɗaden shiga. Su kuma Kristoci 'yan ƙabilar Berom waɗanda ke da rinjaye a wannan jiha na ganin kansu a matsayin 'yan asalin wannan jiha, suna kuma kallon Hausawa da Fulani a matsayin 'yan kaka gida da suka yi musu mamaya suke kuma neman ƙwace madafun iko. A taƙaice dai hakan na nufin cewa ɗan asalin wannan jiha ne kaɗai ya cananci riƙe wani muƙami na shugabanci ko kuma samun tallafi daga hukumar. Solomon Dalung wanda lauya ne kuma masharhanci akan al'amuran yau da kullum ya nasabta wannan rikici da siyasa da kuma ƙarfin tattalin arziƙi. Ya ce ɓangarorin biyu sun yi amfani da addinin ne wajen shawo hankalin mabiyansu da su shiga rikicin. Dalung ya ce babbar laifi anan shine babakere da 'yan ƙabilar Berom suka yi a gwamnatin jihar Filato .

"Tun bayan da 'yan ƙabilar Berom suka amshe madafun iko ne muka gano wata manufa ta mai da sauran ƙabilu saniyar ware domin riƙe madafun iko a arewacin birnin Jos. Hakan dai na da nasaba da rarraba wa matasa filaye da yawa da aka yi. Gwamnati tana ɗaukar matakan yaudarar jama'a da cewa ta mai da hankali ga kau da wannan rikici amma kuma tana yin watsi da hakan. Dalili kenan da ya sa rikicin ya ƙazanta har sai da ya tilasata wa mutane da dama ƙaura daga arewacin birnin Jos."

Dalung wanda shi kansa Krista ne amma ba ɗan ƙabilar Berom ba ya ce gwamnati ta dangata rikicin da addini ne domin samun goyon bayan sauran ƙabilun krista wajen cimma manufarta.

Mafita daga rikicin Filato

Ignatius Kaigama, babban limamin Katolika a JosHoto: DW/T.Mösch

Shi kuma a nasa ɓangaren babban limamin Katolika na wannan jiha. Ignatius Kaigama suka ya yi ga gwamnati jihar da Jonah Jang ke jagoranta da cewa ita ce ke hanzuga rarrabe tsakanin 'yan asalin wannan jiha da wadanda aka kira 'yan mamaya-abin da a cewarsa ya kamata a haramta a Tarayar Najeriya.

Ya ce: " An buƙaci hana wa mutane gina coci ko kuma gudanar da wani shiri akan rediyo da telebijan. Su kuma Musulmai sun yi zargin hana musu gina masallaitai ko kuma samun damar faɗar ra'ayinsu ta kafafen yaɗa labaru. Ana buƙatar hukunta waɗanda ke da alhakin wannan rikicin saboda cewa ta hakan ne kaɗai za mu san cewa mu 'yan uwan juna ne."

Akwai kuma mutane da dama da ke da ra'ayin cewa akwai buƙatar ba wa kotun hukunta miyagun laifuka ta ƙasa da ƙasa damar gudanar da bincike akan kashe-kashe da aka yi a jihar Filato. Fatan babban limamin na Katolila dai shi ne gamayyar ƙasa da ƙasa ta ƙara yi wa gwamnatin Najeriya matsin lamba musamman yayin ziyarar shugabar gwamnatin Jamus a Najeriya.

Ana iya sauraon wannan rahoto da rahoton da wakilinmu Mohammed Bello ya aiko mana akan haɗin-gwiwar aikin makamashi tsakanin Jamus da Najeriya da kuma firar da abokin aikinmu, Saleh Umar Saleh ya yi da Ibrahim Ayagi kan ƙawancen tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafi: Thomas Moesch/Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani