Tasirin rikicin Adamawa a siyasar Najeriya
July 10, 2014Guguwar rikicin siyasar jihar Adamawa da ke ci gaba da daukar sabon salo, tun bayan kafa kwamitin da ke binciken gwamnan jihar da aka yi, binciken da masu fashin baki a siyasar Najeriyar ke danganta shi da kalaman da gwamna Murtala Nyako ya yi a kan batun tsaro a kasar. Hakan dai ya kai ga nuna ‘yar yatsa ga shugaban kasar Goodluck Jonathan, a yanayin da ba kasafai aka saba gani ba a Najeriyar, duk da cewar dimukradiyya ta ba da damar yin hakan.
Kama hanyar fuskantar tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa ke lakada wa kashi, a rikicin siyasar jihar da ya sanya gwamnan fuskantar matsin lamba da ma barazana ga kujerar mulkin jihar bisa matakin tsigewa, ya sanya Sanata Kabiru Gaya na majalisar datawan Najeriyar, bayyana cewa akwai fa bukatar ana sara ana duban bakin gatari.
Ko da yake 'yan majalisar jihar ta Adamawa da ke kara jajircewa a kan yunkurin tsige gwamnan da mataimakinsa sun bayyana batu na cin hanci da rashawa a matsayin dalilansu na tsarkake yadda ake jan akalar gwamnatin jihar da ma dukiyarta, wanda shine babban batu da ke tsole wa kowa idannu, saboda tasirin da kudi ke dashi ga rayuwar bil'adama, amma wasu na fassara rikicin daban.
Tuni dai datawan Adamawar, da ma na wasu sauran sassan Najeriya suka kai dauki domin kwantar da wannan rikicin siyasa, domin tserar da tsarin dimukradiyya da yanayin zamantakewar al'ummar jihar.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar