Amirka: Matsalar rashin kudi ga FBI
January 23, 2019Rahotanni sun nunar da cewa a yanzu hukumar ta FBI, ba ta iya biyan wasu ma'aikatanta da suka hadar da masu kwarmata mata bayanai da masu yi mata fassara, abin kuma da zai iya shafar yakin da Amirkan ke yi da ta'addanci. Wani jami'in hukumar ta FBI da ya nemi a sakaya sunansa ya nunar da cewa, matsalar na da nasaba da dakile wani bangare na kasasfin kudi da mahukuntan Amirkan suka yi. A ranar Alhamis 24 ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne, ake sa ran majalisar dokokin Amirkan za ta tattauna yadda za a kawo karshen rufe wasu ma'aikatun a Amirkan da ya dauki tsahon lokaci. Matakin dai na bukatar amincewar kaso 60 cikin 100 na 'yan majalisar daga bangaren jam'iyya mai mulki ta Republican da kuma ta adawa da ke da rinjaye a majalisar ta Democrats.