1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin sassauta wa Iran takunkumin sayar da mai

Mahmud Yaya Azare
March 20, 2026

A yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya,ke kara yin tkamari shugaban Amurka, Donald Trump, na duba yiwuwar sassauta wa Iran takunkumin sayar da man fetur da aka kakaba wa kasar a baya.

Deutschland 2026 | Iran-US relations. Why can’t they be friends
Hoto: DW

A daidai lokacin da rikici ke kara tsananta a Gabas ta Tsakiya, shugaban Amurka, Donald Trump, na duba yiwuwar sassauta takunkumin man fetir da aka kakaba wa Iran, ana ci gaba da tafka mahawara ga tarisin da matakin zai yi a kasuwar man fetur dama tattalin arzikin duniya.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Iran ke ci gaba da toshe mashigin Hormuz, hanya mai matukar muhimmanci da ake wucewa da kusan kashi 20 cikin 100 na man duniya. Lamarin da ya janyo tsaiko ga zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma tashin farashin man a kasuwannin duniya.

Karin Bayani: Martanin 'yan Iran kan takunkumin Amirka

Tunkuda makamashin mai ta bututu zuwa kasuwannin duniyaHoto: Marty Melville/AFP/Getty Images

Rahotanni sun nuna cewa Amurka na tunanin sakin wasu dubban gangunan man Iran da ke kulle a teku domin rage tashin farashin mai.

Wannan na faruwa ne yayin da Iran ke mayar da martani ga hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.

A yayin da ake ganin matakin sassauta takunkumin na iya kara yawan man da ke shiga kasuwa, wanda zai taimaka wajen rage hauhawar farashin man a duniya.

Karin Bayani: Sabon takunkumi kan Iran

Jirgin dakon mai a kan tekuHoto: Rafiq Maqbool/AP Photo/picture alliance

Sai dai masana irin su Jamal Hateem,na cibiyar binciken tattalin arzikin Gabas ta Tsakiya da ke Masar na gargadin cewa hakan na iya bai wa Iran karin kudaden shiga, wanda zai iya kara karfinta a rikicin da ta ke yi.

A lokaci guda kuma Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare domin bude mashigin na Hormuz, bayan Iran ta yi amfani da jiragen ruwa, wajen harba makamai masu linzami wajen toshe hanyoyin ruwa.

Karin Bayani:Shugaba Trump na duba yiwuwar sassauta wa Iran takunkumi

Wani katafaren tankin mai na AmurkaHoto: Brian Snyder/REUTERS

A takaice,dai shirin Donald Trump na sassauta takunkumin man fetur din na Iran na zuwa ne a wani lokaci mai sarkakiya.

Matakin na iya rage tsadar farashin mai, amma kuma yana dauke da hadarin kara dagula rikicin da ya riga ya yi kamari.

Har yanzu dai shugaba Trump bai yanke wannan shawarar ba.

A yanzu dai duniya na ci gaba da sa ido domin ganin ko zai aiwatar da wannan aniyar ta sa kuma ko wannan mataki zai kawo sauki, ko kuma zai kara rura wutar rikicin

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani