1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Mohamed Tidjani Hassane Carole Assignon, Sandrine Blanchard/SB/MAB
June 29, 2023

Kwanaki kalilan bayan yukurin tawaye da shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner ya yi wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha, mahawara ta barke kan makomar dakarun da ake kyautata zaton sun raba gari da fadar Kremlin.

Masu zanga-zanga rike tutar Rasha a Bangui, fadar gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Masu zanga-zangar goyon byan Rasha a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Barbara Debout/​AFP/​Getty Images/AFP

Kamfani sojojin hayan Rasha na Wagner ya sallama wa Afirka ne a shekarar 2018 da nufin kare muradu da kuma yada manufofin Rasha a wasu kasashen nahiyar.

Dakarun sun fara ne da saka kafa a Afrika ta tsakkiya domin kai wa kasar makamai a lokacin barkewar rikicin 'yan tawaye da suka hana gwamnatin shugaba Faustin-Archange Touadéra sukuni. Daga wannan lokacin ne kasar ta Afirka ta Tsakiya ta kulla alaka da kamfanin domin ba da horo wa sojinta da kuma cinikin makamai kafin daga bisani sun kula yarjejeniyar ta kama wa sojojin kasar yaki da 'yan tawaye masu kokarin kifar da gwamnatin Bangui.

Karin Bayani: Jaridun Jamus: Batun sojojin Rasha a Afirka

Shugaba Faustin-Archange Touadéra ba Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Präsidentschaft der Republik Ruanda

To sai tun tafiya ba ta je ko ina ba, 'yan kasar suka fara ankara da cewar dakarun na Wagner na aikata munanan laifuka da suka hadar da cin zarafin al'umma, da satar arzikin karkashin kasa irin su zinare tare da azabatarwa ko kuma zartar da hukuncin kisa kan wadanda ke numa adawa da tatsar ma'adinan kasar da suke yi. A yayin wata hira da ya yi da DW, Adrien Poussou tsohon ministan sadarwar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a lokacin gwamnatin Michel Djotodia, ya ce Wagner ta samu gidin zama a kasar ne bisa tursasawa da kuma barazana da shugaban kamfanin Yevgeny Prigozhin ya yi wa Shugaba Faustin-Archange Touadéra domin bai wa Wagner damar dibar ganima. Adrien Poussou ya kuma yi karin haske kan wasu yarjeniyoyi da fadar Bangui ta rattaba bisa matsin lamba daga Wagner.

An rattaba wannan yarjejeniya ta birnin Khartoum ne dai a shekara ta 2019 tsakanin gwamnati da 'yan tawaye da nufin shimfida zaman lafiya a kasar a kokarin da gwamnatin Bangui ta fara tun shekara ta 2012.

Masu zanga-zanga a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Carol Valade/AFP/Getty Images

To amma wani labarin da Jaridar Jeune Afrique ta bankado a shekarar bara ya nunar da cewa shugaban kamfanin na Wagner ya wuce gona da iri a Jamhuriyar Afirka ta Tsakkiyar. Hasali ma jaridar ta ruwaito cewa Prigojine ya tursawa gwamnatin kasar amincewa kananan gundumomin kasar su rinka ware wa kamfanin da 'yan tawayen da aka sasanta da su wani kaso na kudadensu.

Duk da mahawarar da ake tafkawa dai kan makomar dakarun na Wagner bayan yunkurin tawayen da shugaban kamfanin Yevgeny Prigozhin ya yi, wanda ke zama alamun raba gari da fadar Kremlin, har kawo yanzu alaka na nan daram tsakanin kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kamfanin sojojin hayan.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani