1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin yakin Amurka a Iran akan wasanni

March 16, 2026

Yayin da yakin Amurka da Isra'ila akan Iran ke ci gaba da gudana, a gefe guda yakin ya yi tasiri akan harkar wasanni a Gabas ta Tsakiya

Gasar kwallon kafa ta mata ta 2026, Karawa tsakanin Koriya ta Kudu da Iran
Gasar kwallon kafa ta mata ta 2026, Karawa tsakanin Koriya ta Kudu da IranHoto: Dave Hunt/AAP/IMAGO

Za mu fara labarin wasannin daga yankin Gabas ta Tsakiya, inda yakin da Iran ke ci gaba da gwabzawa da kawancen Amurka da Isra'ila ya fara tasirin a harkar wasanni a Iran da ma wasu kasashen yankin Gulf.

A karshen makon jiya an buga wasannin mako na 26 na gasar Bundesliga a Jamus inda a jimlace aka zura kwallaye 15 kacal a wasanni tara da aka fafata a filaye daban-daban, adadin da ya gaza kai na wasannin mako na 25, inda aka yi ruwan kwallaye 36.

Za mu fara da wasan karshe da aka rufe makon na 26 da shi wanda aka buga a ranar Lahadi a filin wasa na MHP Arena, inda Stuttgart da ke a matsayi na hudu a teburin gasar ta karbi bakuncin RB Leipzig wadda ke a matsayi na biyar.

Wasan ya yi matukar daukar hankali domin kungiyoyin biyu na neman gurbin zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. A karshen wasan Stuttgart ta samu nasara da ci daya mai ban haushi, kuma dan wasan gaba Deniz Undav ne ya zura kwallon a minti 60 da fara fafatawa. Wannan ne ma kwallo ta 15 da dan wasan ya zura a kakar bana, lamarin da ke nuna cewa yana kan ganiyarsa.

Karin Bayani:Bayern Munich tana kara karfi a Jamus

Bundesliga: Karawar RB Leipzig da VfB Stuttgart Hoto: O.Behrendt/IMAGO

Bayan wannan sakamako Stuttgart na ci gaba da rike matsayi na hudu da maki 50, inda ta ke kunnen doki da Hoffenheim wadda ke a matsayi na uku duk da canjaras da ta yi 1–1 da Wolfsburg.

A gefe guda kuma, RB Leipzig na matsayi na biyar da maki 47, inda ta shiga gaban Bayer Leverkusen da maki biyu wadda ke matsayi na shida.

A wani wasan kuma da ya dauki hankali a Bundesliga, Bayer Leverkusen ta tashi kunnen doki ci 1-1 da Bayern Munich, duk da cewa yaya babba ta kare wasan da ‘yan wasa tara bayan samun jan kati guda biyu.

Tun da farko Leverkusen ce ta fara zura kwallo a minti na shida ta hanyar Alex Garcia, amma bayan cin wannan kwallo, Leverkusen din ta baras da manyan damammaki da za ta iya nade wasan. Wannan ya sa Bayern Munich ta ci gaba da matsa lamba, inda daga karshe dan wasa Luis Diaz ya samu damar farkewa a minti na 69 kafin daga bisani alkalin wasa ya maka masa jan kati a minti na 84.

To sai dai kungiyar Dortmund ta yi anfani da wannan sakamako domin rage ratar maki dake tsakaninta da Bayern Munich bayan ta doke FC Augsburg da ci 2–0.

FC Augsburg da. FC Bayern MünchenHoto: Alexander Hassenstein/Getty Images

Bayan karkare makon na 26, Bayern Munich na ci gaba da jan ragamar teburin gasar da maki 67, yayin da Dortmund ke a matsayi na biyu da maki 58. 'Yan baya ga dangi su ne Heidenheim da Wolfsburg da ke fuskantar hadarin faduwa daga gasar zuwa rukunin 'yan biyu.

A Spain a karshen mako an sabuta wa Joan Laporta wa'adin shugabancin kungiyar kwallon kafar Barcelona, inda ya samu kashi 68 cikin dari na kuri'un da aka kada. Laporta mai shekaru 63 a duniya ya yi alkawarin cewa a sabon wa'adinsa, shugabanni da magoya bayan Barca za su hada kai wajen sake farfado da ruhin kungiyar a nahiyar Turai.

A daidai wannan lokaci ne Barcelona ta yi raga-raga da Sevilla ci 5-2 a wasan mako na 28, lamarin da ya bata damar ci gaba da jan zarenta a kan teburin Laliga da maki 70 cif inda ta bai abokiyar hamayya Real Madrid tazarar maki 4.

Za mu karkare da gasar Premier inda hamayya ke kara zafi tare da daukar sabon salo wajen neman gurbi zuwa gasar zakarun Turai ta kakar wasa mai zuwa.

Ayar tambayar da ake dasawa ita ce: Shin wace kungiya ce za ta samu tikitin shiga gasar zakarun Turai, bayan da Liverpool da Chelsea suka yi tuntube a wasanni mako na 30?

Karawa tsakanin Liverpool da Tottenham Hoto: Paul Ellis/AFP/Getty Images

Ita dai Liverpool ta tashi kunnen doki 1–1 da Tottenham, duk da cewa Tottenham din na cikin mawuyacin hali a kakar bana. Wannan sakamakon ya kara dagula damar Liverpool na kare kakar a cikin kungiyoyi hudu na saman teburin Premier. Bayan kammala wasan, wasu daga cikin magoya bayan Liverpool sun nuna rashin jin dadinsu inda suka fusata tare da yi wa ‘yan wasan ihu. Wannan na zuwa ne bayan yanayi mai wahala da kungiyar ke fuskanta, domin dama dasi a tsakiyar makon jiya ta sha kashi a hannun Galatasaray a gasar Zakarun Turai.

A gefe guda Manchester United karkashin mai horaswa Michael Carrick na ci gaba da yin abin kai, inda ta dare kan matsayin na uku na Premier bayan doke Aston Villa ci 3-1. Sai dai wannan lamari ya jefa Aston Villa cikin matsin lamba a kokarinta na samun gurbi a jerin kungiyoyin da ke sama teburi.

Ita kuwa kungiyar Chelsea abin fallasa ta yi a gida inda ta yi barin maki bayan shan kashi da ci 1–0 a hannun Newcastle.

Wannan sakamako ya haddasa raguwar ratar maki a tsakanin Chelsea da Liverpool, inda a yanzu maki daya ne kacal ke tsakanin kungiyoyin da ke a matsayi na biyar da na shida.

Wasannin mako na 30 dai sun kara birkita lissafi a gasar Premier Ingila, musamman wajen kokawar neman gurbin shiga gasar zakarun Turai. 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani