1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin yakin Iran kan alakarta da Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe ZMA
March 4, 2026

Duk da nisan da ke tsakanin Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya, amma Iran na da alaka a fannonin kimiya da tattalin arziki da kasashen Afirka.

Iran Teheran 2026 | Rauchsäule nach US-israelischem Luftangriff nahe dem Azadi-Turm
Hoto: Hamid Vakili/Parspix/ABACAPRESS/IMAGO

Sakamakon alaka da Iran ta dade da kullawa da kasashe da dama na Afirka musamman na yammaci, da dama da ga cikin'ya'yan wannan nahiya na ci gaba da mai da hankali kan yakin da take da yi da Amurka da Isra'ila

Tsawon shekaru da yawa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kara karfafa hulda da kasashen nahiyar Afirka a fannoni daban-daban kama daga jin kai i zuwa kiwon lafiya da kasuwanci da addini, har ma da kimiyya da kuma uwa-uba fannin ilimi. Hasali ma, fadar mulki ta Tehran tana daukar nauyin daliban Afirka da yawa a jami'o'inta, kuma tana habaka ayyukan hadin gwiwar fasaha da al'adu da kasashe da dama a nahiyar, musamman ma a yammacin Afirka.

Saboda haka ne kasashen Afirka da dama ke sa ido sosai kan yakin da ake gwabzawa tsakanin Iran da kuma Amurka da Isra'ila a daya hannun. Alal hakika ma dai, Jamhuriyar Nijar tana daya daga cikin masu mai da hankali sosai a kan yakin saboda a cikin 'yan shekarun nan, an yada jita-jitar samun danganta  tsakanin Niamey da Tehran game da makamashin uranium, lamarin da ya haifar da muhawara mai yawa.

Hare haren Isra'ila a birnin Beirut na kasar LebanonHoto: Hassan Ammar/AP Photo/dpa/picture alliance

Amma Seidik Abba, mai sharhi, dan jarida, kuma kwararre kan yakin Sahel da Tafkin Chad, ya danganta wannan batu da soki burutsu saboda ba a taba kitsa cinikin makamashin uranium tsakanin Nijar da Iran ba.

"Dangantaka tsakanin Nijar da Iran ta kasance kafin batun uranium. Ya zuwa yanzu, Nijar ba ta sayar da ko kadan daga cikin uraniumta ga Iran ba. Gaskiya ne cewa Iran ta nuna sha'awar sayan uranium na Nijar, a dabarunta na habaka makamashin nukiliya da shirye-shiryen bincikenta. Wasu hasashe ma na nuna buri da suka shafi makaman nukiliya. Amma a halin yanzu, babu wata dangantaka mai karfi tsakanin Niamey da Tehran a wannan fanni. Musanya ta kasance  ta diflomasiyya. Wakilan Nijar sun ziyarci Iran, kuma jami'an Iran suma sun ziyarci Nijar."

Duk da kasancewarta a nahiyar Afirka, amma Iran ba ta kama kafafun wasu kasashen Turai kamar Faransa ko ma Jamus a fannin mu'amala ba, in ji Dr. Salifou Nouhou Jangorzo, malami kuma mai bincike a Jami'ar Maradi. A cewarsa dai, ko da yake ba ta da karfin fada a ji a Afirka, amma Iran ta kasance abokiyar hulda ga kasashen nahiyar da dama.

"Iran na da ofisoshin diflomasiyya a kasashen Afirka 22, lamarin da ke nuna sha'awarta ga nahiyar. Ta hanyar wadannan ofisoshin jakadancin, tana kula da dangantaka a fannoni da dama musamman a fannin tattalin arziki. Sannan Iran na shirya tarurruka akai-akai tsakaninta da Afirka a matakai daban-daban. Akwai kuma wani fanni na al'adu, musamman na addini, wanda ke taka muhimmiyar rawa, inda ta hanyar mabiya Shi'a, Iran ta samun karbuwa a Afirka."

Jimamin mutuwar Ayatollah Ali Khamenei a IraqiHoto: Anmar Khalil/AP Photo/picture alliance

Akwai kuma hadin gwiwar fasaha tsakanin Iran da wasu kasashen Afirka, musamman a fannin samar da jiragen sama marasa matuka. Wannan fanni yana jan hankalin kasashen Afirka da dama.

"Mutane da yawa ba sa jaddada cewa Iran na da kwarewa a fannin jiragen sama marasa matuka. A yau, mun kwana da sanin cewar kasashen Afirka da dama na sha'awar mallakar irin wannan kayan aiki, musamman wadanda ke fuskantar ta'addanci. Ana sayan mafi yawan jiragen sama marasa matuka ne a Turkiyya, amma wasu kasashe suna komawa ga Iran don sayan jiragenta marasa matuka."

Sai dai Seidik Abba, ya ce wannan yakin zai iya rage ko dakushe ko dakatar da ma'amalar hadin gwiwa da ke tsakanin Iran da Afirka, saboda Tehran za ta iya karkatar da mafi yawan albarkatunta na siyasa, soja, da diflomasiyya don shawo kan wannan yakin da ya shafi kasashe da dama.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani