Tasirin ziyarar Paparoma a kan zaman lafiya a Afirka
April 13, 2026
A wannan Litinin (13.04.2026) din ce shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Leo na 16 ya fara ziyararsa a wasu kasashen Afirka, inda ziyarar tasa ta fara da cacar baki tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump bayan da Paparoman ya yi kira kan a kawo karshen yakin da Amurka ke yi a kasar Iran.
Jamhuriyar Kamaru da Angola da Equitorial Guinea da kuma kasar Aljeriya ne ke cikin jerin kasashen da Paparoma Leo din zai ziyarta, kuma wannan ziyara tasa ita ce irinta ta farko a nahiyar Afirka tun bayan da aka ayyana shi a matsayi shugaban cocin Katolika na duniya a shekarar 2025 da ta gabata.
Karin bayani:Fafaroma ya nemi a samar da zaman lafiya a Lebanon
Da sanyin safiyar nan ne dai Paparoman ya isa birnin Algiers na kasar Aljeriya, inda tuni ya kai ziyara zuwa ga wajen tarihin na Maqam Echahid da aka samar da shi a shekarar 1982 domin tunawa da wadanda suka sadaukar da rayuwarsu a lokacin da Aljeriya din fafutukar samun 'yancin kai. Jim kadan bayan sanya furanni don girmama wadanda suka rasu, Paparoman ya ja hankalin al'umma kan muhimmancin zaman lafiya.
"Ina son mu tuna cewar ubangiji na son ganin kowace kasa ta kasance cikin zaman lafiya, zaman lafiyar da zai bayar da dama ta yin adalci da kuma girmama kowa da kowa. Zaman lafiyar da zai sanya mu fuskanci gobenmu da niyar yin yafiya ga kowa maimakon a ce kullum muna cikin tashin hankali."
Wannan sako na salama da Paparoman ya aike da shi ba wai ga al'ummar Aljeriya ko sauran kasashen da zai ziyarta ya tsaya ba, ya aike da makamancinsa ga Amurka da kan yakin da take yi a Iran inda ya soki lamirin yakin tare da yin kiran da a kawo karshensa. Sai dai ga alama shugaban Amurka Donald Trump bai ji dadin wannan sako inda ya fito ya caccaki Paparoman tare da cewar bai ma san me yake yi ba sai dai Paparoman ya ce wannan ba zai hana shi yin kiran da samar da zaman lafiya ba don ba tsoron Trump din yake ba.
Karin bayani:Fafaroma ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinya
To yayin da wannan cacar baka ke wakana tsakanin Paparoma Leo din da Shugaba Trump, sauran kasashen kasashen da za su karbi bakuncin shugaban na Cocin Katolika na cike da shaukin game da zuwansa. mazauna kasar Angola ga misali na ta rajin ganinsa don a ganinsu ziyararsa za ta bude wani babi ne na wanzar da zaman lafiya.
"Muna matukar farin ciki da wannan ziyara da Paparoma zai kawo mana angola don zai zo ne da sakon zaman lafiya da kuma sasanta al'umma. Ziyarar tasa aba ce mai muhammanci gaske wadda ke cike da albarka. Muna son ganin an samu zaman lafiya kuma an sasanta wadanda ke rikici da juna."
Su ma dai al'ummar Jamhuriyar Kamaru irin wannan shauki suke cike da shi, inda Samuel Kleda da ke jagorantar mabiya darikar ta Katolika a birnin Douala ke cewar ziyarar ta Paparoma Leo wata dama ce ta musamman da suka ta samar da sauyi a lamuran su na yau da kullum.
"Ziyarar Paparoma ziyara ce ta musamman da za ta ba mu dama ta gyara tsakaninmu da yanayin zamantakewarmu wanda ba shakka zai taimaka mana wajen samun zaman lafiya mai mana."
Karin bayani: Fadar Vatican ta karbi bakuncin mataimakin shugaban Amurka
To a ranar Alhamis din da ke tafe ne dai Paparoman zai kammala ziyararsa a Equitorial Guinea bayan kammala taro da mabiya Katolika a babban birnin wasa na Malabo fadar gwamnatin kasar inda daga nan ne kuma zai nifo gida Rome.