Tattalin arzikiJamus
Jamus: Fara farfadowar tattalin arziki
January 15, 2026
Talla
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya kaddamar da babban tsarin kashe kudi a kokarin bunkasa tattalin arzikin, sai dai da kyar da jibin goshi aka samu dan ci-gaba, bayan tafiyar hawainiya da tsarin ya yi. Da take karin haske shugabar Ofishin Kula da Kididdiga a Hukumar Kiddidga ta kasar Ruth Brand ta ta alakanta hakan da yadda al'umma ke sayen kayayyaki, da kuma kudin da gwamnati ke kashewa wajen gudanar da ayyuka. Ta kuma nunar da cewa: "Bayan shekaru biyu ana fama da masassarar tattalin arziki a Jamus, yanzu ya farfado.