1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKamaru

Tattalin arzikin Kamaru na tafiyar hawauniya a mulkin Biya

Mouhamadou Awal Balarabe
November 6, 2024

A ranar 6 ga Nuwamba ne Shugaba Paul Biya ke cika shekaru 42 a kan kujerar mulkin Kamaru. Dai dai duk da arzikin karkashin kasa da filayen noma da ta mallaka, amma kashi 23% na al'ummar Kamaru na rayuwa a cikin talauci.

Paul Biya ya kasance daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan mulki a duniya
Paul Biya ya kasance daya daga cikin shugabannin da suka fi dadewa a kan mulki a duniyaHoto: Jemal Countess/UPI/newscom/picture alliance

Paul Biya ya zama shugaban Kamaru a 1982 a lokacin da kasar ke tsaka da samun wadatar tattalin arziki, inda bunkasarta ta zarta kashi 10% a kowace shekara. A wadannan shekaru, ta tsere wa makwabtanta na yankin Tsakiyar Afirka a karfin arziki, inda ake samun kanfanonin kasashen waje da na cikin gida a fannin gandun daji da aikin noma da masana'antar masarufi da siminti da tamma da karafa da sauransu. Amma a yanzu, kasar na dogaro kan cibiyon da ke ta'ammali da kudi irin su Bankin Duniya da Asunsun Ba Da Lamuni na Duniya wajen neman farfadowa daga halin da ta samu kanta a ciki, inda take samun bunkasar kashi 3% zuwa 4% na arziki.

Karin bayani: Ana fama da karancin abinci a Kamaru

Masanin tattalin arziki Louis-Marie Kakdeu, ya ce koma bayan da tattalin arzikin Kamaru ke fuskanta ya kasance abin mamaki, duba da albarkatun da Allah ya hore wa kasar. Ya ce: " A shekarun 1980, tattalin arzikin Kamaru ba shi da matsala. Amma a 2024, an yi wa tattalin arzikin zagon kasa. Wannan ne ya sa ake fuskantar karancin kudin shiga, a kasa mai dimbim arziki kamar Kamaru."

Faduwar farashin koko da fetur ne ke jawo nakasu

Akasarin 'yan kamaru na kananan kasuwanci don samun abin sa wa a bakin salati.Hoto: Henri Fotso/DW

 A shekarun 1990 ne alamun koma bayan tattalin arziki suka fara bayyana a karkashin mulkin Paul Biya, biyo bayan faduwar farashin kofi da koko da man fetur, wanda ya haifar da tabarbarewar harkokin kasuwanci. Sannan, faduwar darajar kudin CFA da Kamaru ke amfani da shi, ya sa gwamnati daukar matakan tsuke bakin aljuhu, ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba. Bankin Duniya ya ce tsakanin 'yan kamaru miliyan 12 zuwa 15 na rayuwa da kasa da 815 Frans CFA a rana,. Sannan akwai karin mutane  miliyan uku da ke bukatar agajin gaggawa na abinci a kasar saboda ba su da aiki da za su iya dogaro a kai wajen samun na sa wa a bakin salati.

Karin bayani: Rashin wutar lantarki a Kamaru

Masanin tattalin arziki Louis-Marie Kakdeu ya ce wasu 'yan Kamatu na samun kansu a cikin mawuyacin halin arziki saboda an mayar da su saniyar ware. Ya ce: " Saboda kawai an cire su daga tsarin tattalin arzikin kasar ne. Ana shaidar da wannan a tsarin bankuna da inshora. Idan 'yan kasa ba sa samun bashi a bankuna don karfafa jarinsu, sannan ba sa samun kare amfanin gonakinsu a kanfanonin inshora ba, to dole ne talauci ya samu gingin zama. Ya wajaba, a magance wannan matsalar don su samu damar amfana da tsarin bankuna tare da fita daga talauci"

Cin hanci na ci gaba da kassara arzikin Kamaru

Paul Biya bai cika fitowa bainar jama'a ba tun bayan da shekarunsa suka turaHoto: Wu Hao/AP Photo/picture alliance

Matsalar cin hanci da rashawa da gwamnatinBiya ta yi kaurin suna a kai ta jawo wa kasar nakasu a fannin tattalin arziki. Ko a  2023, kungiyar Transparency International ta ci gaba da sanya Kamaru a matsayi na 140 daga kasashe 180 na wadanda aka fi kabar rashawa a cikin su, inda ta ce cin hanci ya sa kamaru asarar kudi na CFA biliyan 114, duk da cewa fadar mulki ta Yaoundé ta kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa,.

Stephane Akoa, mai bincike na gidauniyar Paul Ango Ela ya ce hukumomin yaki da cin hanci na da rauni sosai, inda ya ce: " Shawarwarin da wadannan hukumomi ke bayarwa, wadanda ke kunshe a cikin rahotannin da suke wallafawa, ba wajibi ba ne hukumomin kasar Kamaru su karbe su, amma za su iya haifar da ci-gaba a yaki da cin hanci da rashawa, a dukan matakai na rayuwar al'ummar Kamaru."

Karin bayani:  Kamaru: Kalubalen yan jarida da matakin gwamnati

A farkon shekarun 2000, gwamnnatin Paul Biya ta girka wasu dabaru na rage dogaro a kan man fetur da a cewarta za su taimaka wa Kamaru tsayawa a kan kafafunta a fannin tattalin arziki kan nan da shekarar 2035.