1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzikin kasar Senegal

Yahouza SadissouDecember 4, 2005

Kasar Senegal ta yunkura wajen habaka tattalin arzikin ta

Senegal
Senegal

Kasar Senegal dake yammacin Afrika, na da murrabadin kilomita 193.000, da kuma al´umma kimanin million 10.

Abdulahi Wade ,ke shugabancin wannan kasa, tun shekara ta 2000.

Ta fannin tattali arziki,bayan shekara da shekaru na fama da kangin talauci,tu shekaru kimanin 10 da su ka wuce kasar ta fara yunkarawa.

Duk da cewa Senegal ba ta arzikin karkashin kasa mai yawa, kamar wasu kasashen Afrika, Allah ya arzuta ta da albarakar ruwa kasancewar tayi iyaka da teku.

A game da albarkatun noma, kasar ta yi suna matuka, ta fannin noman gyada da na kayan danye, wanda mafi yawan su a ke sayarwa ga kasashen ketare.

Arzikin Phostate da kasar ta malaka, na tallafawa matuka gaya, wajen sarrafa takin zamani domin kara ingatuwar harakokin noma.

Bugu da kari,Senegal na da arzikin man petur, saidai bai taka kara ya karya ba.

Sannan,albakatun kamun kifi, daga teku, da kogin Senegal, na samar da kuddaden shiga masu, yawa ga baitul malin gwamnati, da kuma ciyar dubunan masu kamun kifi na wannan kasa.

A halin yanzu kampanoni da dama na kasashen ketare na ci gaba da bincike a yankunan da a ka gano barbashin taggulla, karafa darma da kuma Gas, wanda a ke sa ran a yan shekaru masu zuwa, za su rtaka mahimiyar rawa, ta fannin bunkasa tattalin arzikin kasar.

A bangaren abin da ya shafi makamashi, baban birnin kasar wato, Dakar ta zama mattatara ta manyan manayan kampanoni da masana´antu, da kuma tashoshin samar da wutar lantarki.

Hada-hadar kasuwa a wannan birnin ta kara samun magogara daga tashar jiragen ruwa da kuma filin asaukar jiragen sama da su ka yi suna a Afrika da kasashen ketare.

Kungiyoyin kasa da kasa, da dama ,na Afrika sun girka cibiyoyin su ,a birnin, dalili da tasirin sa, a harakokin cinikaya na dunia.

Alal misali, Cibiyar babban bankin kasashen Afrika ta yamma na a wannan birni.

Manyan manyan hotel hotel da wuraren shakatawa, da na tarihi na jowo yan yawan bude ido daga dunia baki daya a birnin Dakar.

A baya ga Dakar, Kaolaha da ke matsayin birni na 3, mafi girma a kasar Senegal,na bada gumuwa mai tasiri, ta fannin ci gaban tatalin arzikin wannan kasa.

Saidai ya zuwa birni na fuskantar koma baya ta fannin noman gyada wanda a kan shi ne yayi suna a shekaru baya.

A halin yanzu, manoman yankin sun fi raja´a, ga noman kada massara, da na gero.

A game da haka an kaffa kampanoni da dama, na sarrafa wannan albarkatun noma.

A daya hannun, Kaolaha, na samar da gishiri mai tarin yawa, da kasar ke anfani da shi, a cikin gida da kuma, sayarwa a kasuwanin ketare.

Senegal kamar sauran kasashen Afrika , na huldodin cinikaya

da dunia, saidai kuddaden da ke fita, ta hanyar sayo kaya daga ketare , sun zarta yawan wanda ta ke samu, ta hanyar sayar da hajojin ta a kasuwanin waje.

Alal misali, a shekara ta 2004 a jimilce, Senegal ta sayar da hajoji na kudade kimanin CFA billiard 657.

Wannan hajoji sun kunshi kifi, takin zamani, kada da kuma man petur.

A bangaren kudaden da kasar ta kashe wajen sayen kaya daga ketare sun tashi CFA billiar daya da kussan rabi.

Manyan kasashen da ta hi hulda saye da sayarwa da su, sun hada da India, Faransa, Mali, Nigeria da Ivory Coast.

Mu´amila cinikaya tsakanin Senegal da India, ta shafi kafofin sadarwa na zamani mussaman Internet da na´urorin sallula.

A halin da ake ciki kiddidia ta nu na cewar a baki dayan yakin yammacin Afrika, wannan kasa ke sahun gaba, ta fannin yaduwar wayoyin sallula da Internet.

Idan a ka dauki rukunin kasashen da Senegal ke sayar wa da hajojin ta, a jimilice, kashi 37 % sun shafi Afrika, sannan kasashe turai a saju na 2 ,da kashi 31 bisa 100, sai kuma yankin Asia da kashi 17 bisa 100, a ko wace shekara.

A banagaren kayan da ta ke saye daga ketare, kashi 47 bisa 100 na shigowa daga turai,mussaman daga Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, sannan sai Afrika tare da kashi 21 bisa 100.

A dalili da kyaukyawar mu´amilar kasuwanci tsakanin Senegal da Faransa, yanzu haka akwai a kalla kampanoni 250 na Faransa da ke aiki a birane daban-daban na kasar.

Kazalika, a shekara da ta gabata, Senegal, fiye da sauran kasashen Afrika ta yamma, ta ci moriyar kudaden taimakon habbaka tattalin arziki , daga Faransa na Euro million 35.

To saidai duk da wannan ci gaba da a ka samu kasar Senegal, ta fannin bunksara tattalin arziki har yanzu a kawai sauran rina kaba, a hanyar kautatta rayuwar jama´a.

Kamar dai sauran kasashen Afrika, itama Senegal ba ta kubuta ba, daga matsalolin cin hanci da rashawa.

Duk da cewa a shekara da ta gabata, gwamnati ta girka wani komiti mai yaki da matsalar, ya zuwa yanzu kiddidiga ta nunar da cewa, kashi 40 bisa 100, na hukumomin gwamnati da masu zaman kan su, sun gurbace da cin hanci da rashawa.

Ita ma,Transparency International, a rahoton ta na shekara banna ta kasa, Senegal a sahu na 78, daga jerin kasashe 159, masu fuskantar matsalar cin hanci da rashawa.

Sannan ta fannin jin dadin rayuwar jama´a, kasar na fama da matsalolin kiwon lahia da na makarantu, balle uwa uba talauci da yi katutu a yankunan birane da na karkara.

To saidai duk da haka, za a iya cewa, Senegal ta ciri tuta, ta fannin yunkurawa, domin habaka tattalin arziki, idan aka kwatata ta da sauran kasashen yammacin Afrika.