1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tattalin arzikin Najeriya na GDP ya bunkasa da kashi 3.4%

May 13, 2025

Sanarwar Bankin Duniyar na zuwa a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da hauhawan farashi da aka yi hasashen zai tsaya yadda yake da kashi 20% a cikin wannan shekara ta 2025.

Matatar man fetur na Najeriya da ke Kaduna
Matatar man fetur na Najeriya da ke KadunaHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Wani rahoton Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na cikin gida wato GDP ya karo da kashi 3.4% a shekara ta 2024, wanda ya dara ci gaban da aka samu na bunkasar tattalin arzikin a cikin shekaru 10.

Karin bayani:Karin gangar man fetur da Najeriya ke hakowa 

Rahoton na Bankin Duniya ya bayyana cewa an samu ci gaba a tattalin arzikin kasar ne sakamakon riba da aka samu wajen fitar da danyen mai da kuma ci gaba da ake samu cikin gaggawa ta fannin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire da kuma cibiyoyin hada-hadar kudade.

Karin bayani:Nageriya: Barazanar karin matalauta miliyan 13 

Kazalika bankin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin kasar na GDP ka iya zarta hakan a wannan shekara ta 2025 da kashi 3.7%. Sai dai rahoton ya bayyana cewa an samu koma baya ta fannin bunkasa noma sakamakon tashe-tashen hankula da ake fuskanta a yankin Middle Belt da ya hada da jihohi 14 da ke shiyyar tsakiyar Arewacin Najeriya.