1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin arzkin Angola ya fara farfadowa----

Jamilu SaniJune 15, 2004

Shekaru biyu bayan kawo karshen yakin basasar kasar Angola tattalin arzikinta ya fara bunkasa---

Yan gudun hijirar Angola.
Yan gudun hijirar Angola.Hoto: AP

Duk kuwa da cewar kasar Angola ta fuskanci matsaloli na koma bayan tattalin arziki sakamakon yakin basasa na kusan shekaru 30 data shafe tana fama da shi,irin wanan hali ya jefa alumar wanan kasa ta kudu maso yammacin Africa mai arzikin mai, mai kuma yawan aluma miliyan 13 cikin hali na kangin talauci.

To sai dai kuma bayan shekaru biyu da kawo karshen yakin basasar kasar ta Angola tattalin arzkin kasar ya fara farfadowa a halin yanzu.

A kasar dai ta Angola albarkatun man da Allah ya hore ma ta na samar mata kashi 40 daga cikin dari kudaden shiga na cikin gida,yayin da sauran fanonin maikatun gwamnati ke samar da kashi 80 daga cikin dari na kudaden shiga na kasa.

Haka zalika harkokin cinikaiyar da ake gudanawa na cikin gida ta hanyar gudanar da saye da sayarwa a kann tituna ne ke samar da kashi fiye da kashi biyu cikin uku na aiyukan yi ga alumar kasar.

Wani masanin tattalin arzikin kasar ta Angola mai suna Jose Cerqueira,ya furta cewa kamata yayi a ce arzikin mai da Allah ya horewa kasar Angola zai taka muhimiyar rawa wajen samar da guraban aikin yi ga alumar kasar,to amman kuma lamarin ya sha baban da yadda ake zatonsa,inda harkoki na cinikaiyar cikin gida ya maye gurbin mai arzikin mai wajen samar da aiyukan yi ga alumar kasar ta Angola.

Ta la’akari da yadda tattalin arzikin kasar Angola ke bunkasa a halin yanzu,harkokin rayuwa sun fara inganta ga wata yar kasuwar kasar ta Angola mai suna Aida Felicia dake zaune a garin Huambo na kudancin Angola.

A halin yanzu dai Aida ta fara samun riba mai yawa a cinikin data ke yi na sayar da takin zamani,ta hanyar wani tsari na bada bashin takin da gwamnati ta bulo da shi,wanda kuma hakan kann bata damar sayen takin mai yawa a farashi mai sauki da kann taimaka mata samun ribar da zata iya ciyar da iyalanta.

Yar asalin kasar dai ta Angola Aida Felicia,ta baiyana cewa rayuwarta ta fi inganta fiye da shekarun baya,inda take karbar bashin na takin zamani daga hanun yan kasuwa,ta sayar ta sami riba kana ta mayar da uwar kudin ga dan kasuwar da ya bata wanan haja ta takin zamani,wanda daga karshe kuma ta kann karke ne da samun ribar da bata taka kara ta karya ba.

Allan Cain daractan dake tsara taron bitar bunkasa tattalin kasar Angola,na mai ra’ayin cewar bulo da sabin matakan inganta harkoki na cinikaiya a kasar Angola,zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Angola,bayan da matsaloli na yakin basasa suka haifar da koma bayan tattalin arzikinta.