1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattalin ruwa kalubalen al'umma da shugabanni

March 22, 2017

Ranar 22 ga watan Maris na kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar ruwa ta duniya da nufin yin duba kan matakai da ake bi na samar da isasshen tsabtataccen ruwa da kuma tattalin sa.

Kamerun Flüchtlingslager Minawao
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

A wannan lokaci da mu ke ciki Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akwai mutane sama da miliyan 663 a fadin duniya wanda ke rayuwa ba tare da tsabtataccen ruwan ba, lamarin da ke haifar da cutuka ga miliyoyin mutane. Mutane kan kashe awanni tare da yin tafiya mai nisa da bin layi mai tsawon gaske kafin samun tsabtataccen ruwa na amfanin gida domin kaucewa amfani da gurbataccen ruwa.


Wannan ne ya sa Majalisar Dinkin Duniya ta ware wannan rana domin yin biki da nufin yin duba  kan matakai da gwamnatoci ke dauka na samar da isasshe kuma tsabtataccen ruwa dan rage matsaloli da ake samu sanadiyyar karancin ruwa wanda ake yiwa kirarin abokin aiki.


Taken bikin na bana dai shine "Me ya sa ake barnatar da ruwa"? A wannan bangare na duniya mutane na yin yadda suka ga dama da ruwa duk da matsalolin da ake fuskanta wajen samunsa, jama'a ba sa tattalin sa ta yadda zai wadaci al'ummar.

Hoto: picture-alliance/Pacific Press/R.S. Hussain


Mai Dala'ilu Musa wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum da ke da zama a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ya tabbatar da yadda mutane ke barnar ruwa da aka wahala wajen samun sa. Wasu dai na alakanta yadda yadda mutane ke barnar ruwa da rashin fadakar al'umma muhimmancin ruwa wanda hakkin hakan ya rataya a wuyan hukumomi duk da makudan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen samar da ruwan.


Malam Husaini Garba Sawaba mazaunin layin Goro a unguwan Hausari da ke cikin kwaryar Maiduguri ya na da wannan fahimta.
Kwamishinar kula da albarkatun ruwa ta jihar Borno Dr. Zainab Gimba ta ce gwamnatinsu na daukar matakai da suka dace na ganin an samar da ruwa ga al'umma.

Hoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma


Ana fatan yin amfani da taken bukin bana wajen rage barnar ruwa da ake yi a gidaje da cikin birane dda masana'antu da wuraren ban ruwa da akalla kashi 80% daga cikin dari wanda hakan zai taimaka wajen wadatuwar da kuma alkinta muhalli wanda aka yi imanin zai kyautata lafiyar al'umma baki daya.