Tattara sakamakon zaben kananan hukumomi a Kano
October 26, 2024Talla
A wannan Asabar din ce hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kano ta sanya domin gudanar da zabukan kananan hukumomi.
Sai dai jami'an sanda da sauran rundunonin tsaro na tarayya ba su halarci wuraren zabukan ba domin ba da tsaro, sakamakon umarnin da wata babbar kotun tarayya da ke Kanon ta bayar.
Jami'an hukumar Karota da dakarun Hisbah suke kula da sha'anin tsaro a mazabun inda ya zuwa yanzu aka kammala zaben a wasu cibiyoyi.
Da yake Jawabi bayan kada kuri'arsa gwamnan Kano Abba Kabiru Yusuf ya ce wajibi ne a bai wa jama'a damar cin gajiyar 'yancinsu na zabe ba tare da katsalandan ba.