1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattauna rikicin Libiya a Berlin.

Gazali Abdou TasawaJune 10, 2015

Taron wanda Majalissar Ɗinkin Duniya ta shirya na da gurin sassanta ɓangarorin hamayyar ƙasar ta Libiya da nufin kafa gwamnatin hadin kan ƙasa.

EU Außenminister Treffen
Hoto: picture-alliance/epa/O. Hoslet

Majalissar Ɗinkin Duniya ta buɗe wani zaman taron kan batun ƙasar Libiya a birnin Berlin.Taron wanda ya samu halartar wakillan ƙasar Libiya 23 da kuma na wasu manyan ƙasashen duniya, na da ɓurin ɗaukar matakan samar da zaman lafiya a ƙasar Libiya da zumar hana mata wargajewa a cewar ministan harakokin wajen ƙasar Jamus Frank-Walter Steinmeier a cikin wata sanarwa da ya gabatar a zauran taron.

Taron na Birnin Berlin na kuma da ɓurin ganin bangarorin da ke hamayya da juna a ƙasar ta Libiya sun amince ga saka hannu a kan wata yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗa kan kasa da aka cimma a taron da ya wakana a ƙasar Maroko kan batun ƙasar ta Libiya.