Tattaunawa a kan shirin nukiliyar Iran
October 15, 2013Manyan kasashen da ke da karfin fada a ji a duniya na dab da shiga wata sabuwar tattaunawa a wata cibiyar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva a wannan Talatar (15. 10. 13), domin gudanar da taron yini biyu a kan shirin nukiliyar Iran wanda a ke takaddama a kansa. Wannan kuwa na zuwa ne a dai dai lokacin da masu ruwa da tsaki cikin lamarin, ke kara yin matsin lambar neman cimma maslaha a kan batun, tare da sabuwar gwamnatin Iran mai matsakaicin ra'ayi. Sabon shugaban na Iran, Hassan Rouhani dai, na fatan samun ci gaba a takaddamar, domin bada damar cire wasu daga cikin takunkumin da kasashen duniya suka sanya wa kasarsa musamman ta fuskar tattalin arziki.
Sai dai kuma ana jajiberin taron ne, dukkan bangarorin biyu, suka ce babu wata alamar samun ci gaba mai ma'ana hatta a wannan jikon. Ministan kula da harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif na daga cikin wadanda za su halarci taron, tare da wakilan kasashen Amirka da Faransa da Rasha da Birtaniya da China da kuma Jamus. Iran dai ta jaddada cewar shirin nukiliyarta na zaman lafiya ne yayin da kasashen yammacin duniya kuwa ke cewar na samar da makaman nukiliya ne.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu