Tattaunawa akan Shirin Nukiliyar Iran ta ci tura
June 18, 2012Wakilan kasar Iran da na kasashe biyar masu ikon hawa kujerar na ki a komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus sun tattaunawa a birnin Moscow na kasar Rasha akan shirin nukiliyar Iran amma ba tare da cimma matsaya guda ba. Bangarorin biyu kowanensu ya dage bisa matsayinsa da kuma yiwuwar dakatar da tattaunawar. Kasar ta Iran dai ta tsaya kai da fata cewa manufar shirinta na nukiliya ita ce samar da makamashi domin dalilai na aikin magani.
Iran ta bukaci a sauke takunkumin da aka kakaba mata a matsayin sharadinta na ba jami'ai izinin kai ziyara a tashohinta na nukiliya domin gudanar da bincike. Su dai kasashen yamma sun yi fatali da wannan bukata. Kungiyar Tarayyar Turai ta tabbatar da yin aiki da takunkumin hana sayen fetur daga Iran somi da ranar daya ga watan Yuli mai kamawa. Ita dai Iran ana zargin ta ne da fakewa da shirinta na nukiliya domin kera makaman kare dangi.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Zainab Mohammed Abubakar