1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa da Amurka ba za ta amfani Iran ba — Khamenei

September 23, 2025

Jagoran na addinin Iran ya ce kasarsa bata da niyyar mallakar makaman nukiliya kamar yadda Amurka ke tunani.

Dangantaka tsakanin Amurka da Iran dai ta kara tabarbarewa ne bayan da Washington ta taimaka wa Isra'ila wajen yaki da Iran a cikin shekarar nan ta 2025.
Dangantaka tsakanin Amurka da Iran dai ta kara tabarbarewa ne bayan da Washington ta taimaka wa Isra'ila wajen yaki da Iran a cikin shekarar nan ta 2025.Hoto: Office of the Iranian Supreme Leader/AP/picture alliance

Jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya fada cewa tattaunawa da Amurka ba za ta amfani Tehran ba.

A cikin wani sakon bidiyo da aka yada, Khamenei ya kuma ce Iran ba za ta "mika wuya ga matsin lamba” ba dangane da tace sinadarin uranium dinta.

Jagoran Addinin Iran ya fito bainar jama'a bayan rikicin kasarsa da Isra'ila

Ya kuma sake maimaita matsayar Iran ta cewa kasar bata bukatar makaman nukiliya kuma ba ta da niyyar kera su.

Kalaman na Khamenei sun zo ne a lokacin da shugaban kasar ke halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 80 da ke gudana a New York na Amurka.

Ko za a daidata kan makamashin nukiliyar Iran?

Dangantaka tsakanin Amurka da Iran dai ta kara tabarbarewa ne bayan da Washington ta taimaka wa Isra'ila wajen yaki da Iran a cikin shekarar nan ta 2025.