Shin mai abu ne ya rantse, mara abu ya rantse a siyasar Najeriya musamman ma jam'iyyar ADC da ke adawa? Duk da kotun kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban jam'iyyar ADC, har yanzu Nafi'u Bala na ci gaba da ikrarin cewa shi ne shugabanta.