1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa da tsagerun Niger Delta ta ci tura a Najeriya

Muhammad Bello/YBJuly 4, 2016

Tattaunawar da ke gudana tsakanin bangaren gwamnatin Najeriya da 'yan bundigar yankin Niger Delta ta fada rudani, inda yanzu 'yan bundigar suka koma bude wuta.

Niger Kämpfer
'Yan fafutikar na Niger Delta dai sun matsa kai hare-hare a kadarorin gwamnati da na kasashen wajeHoto: picture-alliance/dpa

Gwamnati dai ta ce har yanzu ta gaza sanin kungiyoyin 'yan bundigar da za a tattauna da su, bisa la'akari da yadda wadannan kungiyoyi ke ta bullowa dabam-dabam.

A wannan Litinin kungiyar Niger Delta Avengers ta ce ta kai jerin hare-hare har biyar a kan kamfanonin man Chevron da NNPC a yankin, kuma ta ce za ta cigaba da kai hari. Hare-haren dai sun zo ne a daidai lokacin da ake tunanin cewar akwai yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kungiyar dai ta Avengers da tafi kaurin suna a yanzu, ta nunar da cewa ba ta taba wani zaman tattaunawa da wakilan gwamnati ba, inda kuma gwamnatin kasar ke nuna cewa kawo yanzu ta gaza tantance bangaren 'yan bundigar da za a ainihin tattauna da su, a sakamakon yadda kungiyoyin 'yan bundigar ke dada bullowa a yankin.

Shugaba Buhari dai na fama da tarin matsaloli kan rikicin da Najeriya ta shigaHoto: DW

Wani da ke da jibi da wadannan 'yan fafutika masu kai hare-hare da kuma bai yarda da bayyana sunansa ba, ya bayyana wa wakilin DW a yankin cewar lallai kam gwamnatin tarayya ta yi ta ganawa da bangarori da dama a yankin, sai dai kuma fa ba wai da kungiyar ta Avengers ba.

A wani yanayi me nuna cewar al'amarin tsaro a sassan ayyukan na mai cikin surkukin ruwayen na Niger Delta ya sake damewa, shi ne na sanarwar kamfanin aikin mai na Agip da safiyar Litinin, cewar wasu 'yan bundiga a cikin surkukin yankin na shiyyar garin Nembe sun bundige wasu Jami'ansu uku har lahira, kuma wasu a cikin Jami'an sun jikkata matika.

Yanzu dai in har wadannan hare-hare suka ci gaba, to labudda akwai nakasu ga sanarwar da gwamnati ta yi a satin da ya gabata, na cin alwashin tunkarar ayyukan hako danyan mai gadan-gadan.