Tattaunawa game da shirin nukiliyar Iran ta yi armashi
April 14, 2012Jakadun manyan kasashe shida masu cigaban tattalin arziki na duniya sun gana a yau da jami'an Iran a birnin Istanbul na kasar Turkiya game da shirinta na nukiliya. Wani jakadan tarayyar Turai a tattaunawar wanda ya bukaci a saya sunansa yace a wannan karon tattaunawar ta yi armashi sabanin wadanda suka gabata. Ana kuma fatan gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar a nan gaba. Fiye da shekara guda kenan da tattaunawa ta ci tura tsakanin Iran da kasashen na yammacin turai akan takaddamar nukiliyar Iran. Ganawar da jakadun manyan kasashen shida wadanda suka hada da Amirka da Birtaniya da Faransa da Rasha da China da kuma Jamus suka yi da jami'an Iran na da nufin samo hanyoyin warware takaddamar nukiliyar ta hanyar diplomasiyya. Iran dai ta dage cewa bata da burin kera makamin kare dangi kuma shirin nukiliyarta na lumana ne, sai dai kasashen yammaci suna fargabar bunkasa sinadarin Uranium da Iran ke yi yana iya kaiwa ga kera makamin na Atom a asirce.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh