Tattaunawa kan rikicin Taliban
August 27, 2013A yau Talata ce shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da Firaministan Pakistan Nawaz Sharif za su cigaba da ganawa a rana ta biyu kan lalaubo bakin zaren waware rikicin 'yan kungiyar nan ta Taliban da ke gwagwarmaya da makamai.
A jiya ne dai shugaba Karzai ya fara tattaunawa da Firaministan Pakistan din a Islamabad inda ya bukace shi da ya agaza masa wajen ganin an kawo karshen tada kayar bayan da 'yan Taliban din ke yi musamman ma dai ta hanyar jawo su kan teburin sulhu da gwamnatinsa.
To sai masu sharhi kan lamuran tsaro a yankin na ganin cewar abu ne mai wuya Pakistan ta iya taka wata rawa ta a zo a gani game da kashe wutar rikicin saboda ana zargin wasu 'yan kasar da taimakawa 'yan Taliban din da kudi da ma maboya a gwagwarmayar da suke yi, yayin da shi kuma Firaministan Pakistan din ya bada tabbacin kaiwa ga ci.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammed Awal Balarabe