Ci gaba da tataunawa kan makamashin nukiliyar Iran
April 24, 2015Talla
Mai shiga tsakani a tattaunawa kan batun nukiliyar kasar Iran tsakanin ta da kasashe shida masu karfin fada a ji a duniya Abbas Araqchi ya ce ana samun ci gaba a tattaunawar tasu ko da ya ke har yanzu bai kai ya kawo ba. Araqchi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai, inda ya ce matakin farko na tattaunawar na yin tafiyar hawainiya, sai dai ya ce kasashen nahiyar Turai da Amirka sun yi kokari wajen warware batun dagewa Iran din takunkumin karya tatalin arzikin da suka kakaba mata. Kasashen Rasha da China da Birtaniya da Amirka da Faransa da kuma Jamus na kokarin ganin sun cimma yarjejeniya da Iran din kan shirinta na nukiliya kafin cikar wa'adin karshe da aka diba musu na nan da karshen watan Yunin wannan shekara.