1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Tattaunawar Amurka da Iran ta kankama a Pakistan

April 11, 2026

Majiyoyi daga gwamnatin Pakistan sun ce tattaunawar na gudana cikin mutumci da fahimtar juna a tsakanin tawagar Amurka da ta Iran.

An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a Pakistan
An fara tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a PakistanHoto: Pakistan's Prime Minister Office/AFP

Rahotanni daga yankin Gabas ta Tsakiya na cewa an yi zagaye biyu na ganawa a tsakanin tawagogin Amurka da na Iran a birnin Islamabad na kasar Pakistan, yayin da ake sa ran gudanar da zagaye na uku da yammacin ranar Asabar ko kuma zuwa safiyar Lahadi.

Gidan talabijin din gwamnatin Iran IRIB ne ya ruwaito hakan, idan ya kara da cewa akwai yiwuwar tawagogin na Washington da  na Teheran su sake zama a wani zagaye na tattaunawar da duniya ta zuba wa ido.

Wani babban jami'i a fadar mulki ta White House ya bayyana cewa ana gudanar da tattaunawar ce kai tsaye a tsakanin bangarorin biyu da kuma mai masaukin baki Pakistan. Wannan na zama karon farko da Amurka da Iran ke yin ganawar keke da keke ba tare da shinge ba tun bayan juyin-juya halin Musulumci na shekarar 1979. 

Bugo da kari wani wani babban jami'i a gwamnatin Pakistan ya bayyana cewa tattaunawar na wakana cikin mutumci da fahimtar juna a tsakanin tawagar Amurka wadda mataikin Trump JD Vance ke jagoranta, bisa rakiyar babban manzon Washington a yankin Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff da surukin Trump Jared Kushner.

A hannu guda kuma tawagar Iran na karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf.