1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawa ta musamman kan Siriya

June 1, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta gudanar da wata zama ta musamman dan neman shawo kan rikicin Siriyar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa

NEW YORK, April 5, 2009 (Xinhua) -- The U.S. Ambassador to the United Nations Susan Rice addresses the media prior to an emergency Security Council meeting called by Japan on April 5, 2009 at UN headquarters in New York after the rocket launch of the Democratic People's Republic of Korea (DPRK). Xinhua /Landov
Susan RiceHoto: picture alliance / landov

Kwamitin kula da haƙƙin bil adama na Majalisar Ɗinkin Duniya zai gudanar da wata zama ta musamman kan Siriya a wannan Juma'ar, wuni guda bayan da gwamnati ta zargi 'yan ta'addan da ke adawa da gwamnati da kisan kiyashin da ya afku a makon da ya gabata a ƙauyen Haula. Gwamnatin ta Damascus ta ƙaryata zargin cewa da hanunta a mutuwar wasu fararen hula 108 bayan da ta gudanar da wani bincike.

Haka nan kuma ta yi zargin cewa mayaƙan 'yan tawayen ƙasar 800 ne suka tabka wannan ta'asa, a yunƙurinsu na shafawa gwamnatin kashin kaji, da nufin ƙara tunzura rikicin da har yanzu an kasa samar masa da maslaha. Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniyar Susan Rice, ta mayar da martani ranar alhamis inda ta ce rahoton da suka gabatar ba wani abu ba ne illa ƙarya, kuma yanzu ya ragewa Majalisar ta ɓullo da wata sabuwar dabara.

"Yanzu zaɓi guda ne ƙadai mambobin al'ummar ƙasa da ƙasa ke da shi, na yanke shawarar ko a shirye su ke su ɗauki wani mataki wanda ya saɓawa shirin Kofi Anan da kuma hurumin wannan Kwamiti"

Tun bayan afkuwar wannan kisa na Haula Majalisar Ɗinkin Duniya ke ɗora alhakin artabun a kan dakarun da ke goyon bayan shuga Basahar Al-Assad, To sai dai yau ne wa'adin da 'yan adawan Siriyar suka ɗebawa gwamnati na amincewa da shirin Kofi Annan ke cika.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar