1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana neman mafita kan rikicin siyasar Sudan

Suleiman Babayo
May 13, 2019

Masu zanga-zanga da sojojin da ke mulki a Sudan sun sake komawa kan teburin neman mafita kan kafa gwamnatin wucin gadi bisa mayar da kasar karkashin mulkin fararen hula.

Afrika | Protests im Sudan
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/M. Hjaj


Sojojin da ke rike da madafun iko a Sudan tare da masu zanga-zanga sun sake komawa kan teburin tattaunawa, domin samun mafita kan kafa gwamnatin wucin gadi kan shirin mayar da mulki ga farar hula.

Shugabannin masu zanga-zangar sun komawa tattaunawar bayan lamura sun kakare, kan rashin samun mafita kafa gwamnatin wucin gadi.