1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar ƙasashen duniya da Iran

May 23, 2012

Shugabannin wasu ƙasashe guda shida na duniya na kwamitin didin na MDD na gudanar da taro a birnin Bagadaza na Iraki dangane da batun shirin nukliya na Iran

ARCHIV: Ein iranischer Techniker arbeitet in der Uranverarbeitungsanlage nahe der Stadt Isfahan (Iran) (Foto vom 03.02.07). Eine Abordnung ranghoher Delegierter der Internationalen Atomenergiebehoerde (IAEA) besucht vom Sonntag (29.01.12) bis Dienstag (31.01.12) im Zusammenhang mit dem Atomprogramm der Islamischen Republik den Iran. Es handelt sich um eine diplomatische Mission. Die IAEA wollte auf Nachfrage keine genaue Zahl der Delegierten nennen und machte keine Angaben dazu, mit wem die Delegation zusammentrifft und ob einzelne Atomanlagen besichtigt werden sollen. Das Ziel der Mission ist es laut Pressemitteilung, "alle ausstehenden, grundlegenden Angelegenheiten zu klaeren". (zu dapd-Text) Foto: Vahid Salemi/AP/dapd
Hoto: dapd

Amirka ta dage cewar tilas ne a dakatar da shirin sarafa makamin nukliyar na Iran,kuma yunƙurin da shugaba Barack Obama na Amirka ya ke na ƙara matsa ƙaimi na ganin an dakatar da shirin nukliyar na Iran na zuwa ne gabannin zaɓen shugaban ƙasar da ake shirin gudanarwa wanda shugaban ke hamzarin yin amfanin da wannan dama domin ƙara samun nasarori da zasu ƙara farijinin sa a wajan masu kaɗa ƙuria'a.

Ko da shi ke tun can da farko a ƙarshen ziyara da ya kai a birnin Teheran shugaban hukumar ta samar da makamashi na duniya Yukiya Amano ya ce ana daf da cimma yarjejeniya da ƙasar ta Iran akan batun , to amma Amirka ta yi gargaɗin cewar ba za a yi riga malam masallaci ba matuƙar ba a ga a zahiri irin abinda ƙasar ta kan iya yi ba.Amurkan dai na ƙara samu matsin lamba daga Isarai'la dangane da wannan batu wacce ta ke ganin an ɓata lokaci so sai wajan ɗaukar matakai akan Iran ɗin da ke zaman babbar barazana dangane da shirin ta na nukliya wanda kuma suke da shakku akan rashin sahihanci takunkumin karya tattalin arziki da aka ƙaƙabawa ƙassar.

Amirka na buƙatar a ƙara matsa lamba ga Iran

Israila dai ta nuna gajen dangana dangane da yadda har aka kasa yin amfani da ƙarfin dawo dawo a kan Iran saboda shirin to amma kakakin fadar White Hous ya ce ba za a yi garaje ba.''ya ce ba mu kai fagen da za a yi amfani da matakin soji ba a yanzu.Shi kan sa ministan tsaro na ƙasar Isra'ila Ehud Barak ya yi gargaɗin cewar taron n ya kamata ya dage domin kada a yi dogaro da tayin da Irakin za ta gabatar na yin alƙawuran dakatar da shirin domin a yi ma ta sassauci.Kuma du dama cewar shugaba Obaman ya sanar da cewar ƙaidoji da ƙasashen duniyar suka giciyawa ƙasar Iran na dakatar da sarafa makamashin nukliyar da kashi 20 tare da rufe wata cibiyar Qom sun yi kaɗan amma shugaban ya na yin sara ya na dubin bakin gatari.''ya ce idan na dubi yadda wasu ke tunani a ɗarma ɗamara yaƙi da Iran ina ganin ya kamata a yi tunanin iri asarar' da abin ka iya janyo wa don haka a yanzu muna bin su da lalama.

Man'yan sepetocin hukumar IAEAHoto: AP

Iran ta dage kan cewar shirinta na nukliya na amfanin farar'hula ne

Ƙasar dai ta Iran ta ci gaba da dagewa akan bakan ta cewa shirin na ta na amfanin fara hula ne ba wai na yaƙi ba kamar yadda ƙasahen duniya suke nuna damuwa na yi war malakar makamin Atom ga ƙasar ba.A wannan saduwa dai ana sa ran ƙasashen zasu yi ƙoƙarin shawo kan :ƙasar ta Iran ta rage sarafa makamashi da kashi 20 cikin ɗari tare kuma da ba da haɗin kai ga hukumar ta samar da makamashin nukliyar na duniya masamman ga manyan sepeto cin ta domin su riƙa gudanar da bincike lokaci zuwa lokaci a ƙasar ta Iran.Masu lura da al ´amuran yau da gobe na hasashen cewar ya na da wahala a kai ga cimma sulhu a wannan taro da ke gudana wanda tuni aka fara samun saɓannin tsakanin manyan ƙasashen wajan dakatar da shirin nukliyar.

Ali Akbar Salehi ministan harkokin waje na IranHoto: AP

Daga ƙasa za a iya sauraron sautin annan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Halima Balaraba Abas