1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shirya taron tattaunawa a Mali

Suleiman Babayo ATB
January 27, 2024

Gwamnatin mulkin soajn kasar Mali da ke yankin yamamcin Afirka ta kafa wani kwamati da zai shirya tattaunawa ta kasa domin tabbatar da zaman lafiya da kungiyoyin 'yan aware na arewacin kasar.

'yan tawaye a yankin Kidal na Mali
'yan tawaye a yankin Kidal na MaliHoto: SOULEYMANE AG ANARA/AFP/Getty Images

Gwamnatin mulkin sojan kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka ta kafa wani kwamiti da zai shirya tattaunawa ta kasa bayan watsi da yarjejeniyar zaman lafiya ta shekara ta 2015 da ta taimaka wajen samar da zaman lafiya da kungiyoyin 'yan aware na arewacin kasar. Kasar Aljeriya ta taimaka aka kulla wancan yarjejeniyar domin samar da zaman lafiya a yankin arewacin kasar ta Mali.

Tun shekara ta 2020 aka fara samun sauye-sauye a kasar ta Mali lokacin da sojoji suka kwace madafun ikon kasar, tare da kawo karshen aikin dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, kana kasar ta bukaci taimakon Rasha.